Duk da matsalolin wutar lantarki da ake fama da su a Nijeriya, kasar ta samu kudin shiga na sama da Naira biliyan 181 daga wutar lantarki da ta sayarwa kasashen waje a shekarar 2024.
Rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS), ya nuna cewa tsakanin watan Janairu zuwa Satumba, Nijeriya ta tura wutar lantarki zuwa ƙasashen Togo, Benin, da Jamhuriyar Nijar, inda aka samu Naira biliyan 181.62.
- Firaminista Li Qiang Ya Shugabanci Taron Majalisar Gudanarwar Kasar Sin
- Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Aniyar Amurka Ta Sanya Karin Haraji Kan Wasu Hajojin Sin Dake Shiga Kasar
A cikin watanni uku na farkon shekarar, ƙasar ta samu Naira biliyan 58.65 daga wutar da aka sayar.
Wannan ya karu zuwa Naira biliyan 63.28 a rubu’i na biyu, sannan aka samu Naira biliyan 59.69 a rubu’i na uku.
Hukumar ta ce, kamfanonin rarraba wutar lantarki sun samu Naira biliyan 391.71 daga abokan huldar cikin gida, wadanda adadinsu ya kai miliyan 12.99 a rubu’i na biyu na shekarar 2024.
Daga cikin wadannan kwastomomi, miliyan 5.92 suna amfani da mita, yayin da miliyan 7.07 ke biyan kuÉ—in wuta ta kiyasi.
Ga yadda wasu manyan kamfanonin samar da wuta suka samu kudi:
- Ikeja (IEDC): Naira biliyan 80.17
- Eko (EKEDC): Naira biliyan 68.03
- Abuja (AEDC): Naira biliyan 63.97
- Ibadan (IBEDC): Naira biliyan 39.58
- Benin (BEDC): Naira biliyan 30.84
- Fatakwal (PEDC): Naira biliyan 29.50
- Enugu (EEDC): Naira biliyan 27.11
- Kano (KEDC): Naira biliyan 19.28
- Jos (JEDC): Naira biliyan 15.54
- Kaduna (KDEDC): Naira biliyan 13.23
- Yola (YEDC): Naira biliyan 4.49