Hukumar Gano Man Fetur ta Kasa (NOSDRA) ta bayyana cewa Nijeriya ta yi asarar naira biliyan 118.864 a cikin watanni biyu na farko na 2025, sakamakon gurbacewar iskar gas.
Wannan na zuwa ne yayin da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Bagudu ya ce gwamnatin tarayya tana amfani da dabarun gida don cimma burinta na sauya makamashi.
- Rage Farashin Man Fetur Na Dangote Ya Sa Wasu Gidajen Mai Na Kullewa
- ISWAP Sun Kai Hari Sansanin Sojoji A Yobe
A cikin rahoton da ta yi na Janairu da Fabrairu 2025, NOSDRA ta bayyana cewa naira biliyan 118 da aka rasa a cikin watanni biyu na farko na shekara yana wakiltar kashi 31.48 na jimillar adadin da aka rasa sakamakon gurbacewar iskar gas a cikin lokacin.
A cewar hukumar, kamfanonin mai da iskar gas da ke aiki a kasar sun samar da iskar gas na naira biliyan 22.3 daga ayyukansu na teku.
Hukumar ta lissafa asarar ta amfani da Babban Bankin Nijeriya (CBN) na musayar canji na naira 1,520 zuwa dala daya.
Hukumar kula da muhalli ta lura cewa yawan iskar gas da ya tashi daga bangaren teku na masana’antar a watan Janairu da Fabrairu, ya ba da gudummawar tan miliyan 1.2 na iskar ‘carbon diodide’ zuwa sararin samaniya, tare da samar da wutar lantarki na Gigawatts 2,200, yayin da kamfanonin da suka kunna iskar gas ke da alhakin takunkumin dala miliyan 44.7 (Naira biliyan 67.944).
A daidai wannan lokacin a cikin 2024, kamfanonin mai da iskar gas da ke aiki a bakin teku sun fitar da iskar gas 29.2 BSCF, darajar dala miliyan 102.3 (N155.496 biliyan); tare da takunkumin da aka biya na dala 58.4 (N88.768 biliyan); fitar da carbon diodide’ na tan miliyan 1.6 da yuwuwar samar da wutar lantarki na 2,900 GWh.
Hukumar ta bayyana cewa jimlar 71.0 BSCF na iskar gas da kamfanonin mai da iskar gas suka fitar a cikin watanni biyu na 2025 sun ba da gudummawar tan miliyan 3.8 na iskar ‘carbon diodide’ zuwa sararin samaniya; kuma yana da damar samar da 7,100 Gigawatts na wutar lantarki.
“Kamfanonin da suka gaza suna da alhakin biyan takunkumi na dala miliyan 141.9, kimanin naira biliyan 215.688,” in ji rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp