Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kwamitin da zai sanya ido kan karbar bakuncin taro karo na hudu kan kanana da matsakaitan sana’oi na kungiyar tarayar Afirka wato AU da za a gudanar a kasar nan.
Za a gudanar da taron ne, daga ranar 23 zuwa ranar 27 a watan Yunin shekarar 2025, a babba birnin tarayyar Abuja.
- Ko Kun San Dalilin EFCC Na Kama Gudaji Kazaure
- Sabbin Fasahohin Noma Na Zamani Na Ci Gaba Da Bayyana A Kasar Sin
Taken taron shi ne, inganta gudanar da kananan da matsakaitan sana’oi ta hanyar amfani da fasahar zamani da kuma samar da damar shigar da kaya a kasuwanni tare da samar da kudaden da za su tallafawa kanana da matsakaitan sana’oi a nahiyar Afirka.
Bayanin hakan, na kunshe ne a cikin sanarwar da Stanley Nkwocha, mai magana da yawaun Mataikain Shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa, wasu daga cikin ayyukan da kwamtin zai gudanar sun hada da, tabbatar da gudanar da kyakyawan tsari, musamman domin a samu cin nasara a karbar bakuncin da Nijeriya za ta yi.
Kazalika, sanarwar ta sanar da cewa, ana bukatar kwamtin ya sanya ido wajen ganin an gabatar da kasidu da alkalan da za su yi hunci kan bayanan da za a tattauna a wajen taron da baje kolin kanana da matsakaitan sana’oi da za a yi a wajen taron tare da kuma mika kyaututtuka ga ‘yan kasuwar kasar da suka dace, a wajen taron.
Acewar sanarwar, Mataimakin Shugaban Ma’aikata da ke a ofishin Mataimakin Shugaban kasa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne, zai shugabaci kwamtin.
Sauran ‘ya’yan kwamtin sun hada da, Ministar Ma’aikatar Kasuwanci da zuba hannun jari Dakta Jumoke Oduwole; Ministan sadarwa da kere-kere da kuma tattalin arziki na fasahar zamani Dakta Bosun Tijani; Ministar yawon bude ido da kirkiren tattalin arziki Hannatu Musawa da kuma karamin Ministan Kasuwanci da zuba hannun jari Sanata John Owan-Enoh.
Sauran su ne, Babbar Darakta ta Hukumar NEPC Madam Nonye Ayeni; Babban Sakatariya ta Hukumar NIPC Madam Aisha Rimi; Manajin Darakta na Bankin Masana’antu Dakta Olasupo Olusi; Shugaban Hukumar FIRS Mista . Zacch Adedeji da sauransu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp