Tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, nan ba da jimawa ba, Nijeriya za ta shawo kan kalubalen da ya dabaibayeta.
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Arewa ta tsakiya a Abuja.
- Nan Da Makonni Uku Ɗalibai Za Su Fara Karɓar Bashi Daga Gwamnatin Nijeriya
- Gwamna Dauda Ya Bayyana Alhinin Mutuwar Shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe
“Babu shakka akwai ‘yan adawa, ba za mu ci gaba da sauraron batutuwan masu suka ba.
“Wadanda ba ’yan jam’iyya ba ne na gaske, masu son ganin jam’iyyarmu ta fada cikin rudani, ba mu da lokacinsu, mu mutane ne, ‘yan siyasa masu kishin kasa.
“Wdannan soke-soken da ake kaiwa shugaban kasa, game da halin da kasar ke ciki, mun yi imanin cewa, nan ba da jimawa ba za mu fita daga cikin wadannan matsalolin.
“Dole ne mu gode wa shugaban kasa kan sabon shirin fatansa; kokari, jajircewa kuma muna tabbatar masa cewa, muna goyon bayansa dari bisa dari,” inji shi.
Tun da farko, Sen. Ameh Ebute, tsohon shugaban majalisar dattawa da ya jagoranci tawagar, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya ga Ganduje kan salon shugabancinsa a jam’iyyar.