Mai magana da yawun shugaban tarayyar Najeriya Garba Shehu, ya ce gwamnatin su na yin duba na tsakani, game da dabarun zamanantar da kasa da Sin ke aiwatarwa, wanda kuma ya kai kasar ta nahiyar Asiya, ga samun gagarumin ci gaban tattalin arziki a duniya.
Garba Shehu, wanda ya bayyana hakan, yayin wata zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce Najeriya ta lura da moriyar da za ta samu daga kwaikwayon dabaru irin na Sin, wadanda suka kai ta ga samun saurin habakar tattalin arziki, har ta kai ga zama daya daga kasashen dake sahun gaba a bunkasuwar tattalin arziki, bisa ga yadda take dukufa a kan zamanantar da harkoki, da ingiza gina ababen more rayuwa.
Jami’in ya kara da cewa “A da akan yi tunanin kasashe masu girma irin kasar Sin ba za su iya cimma muradun su, da zamanantar da kan su ba”.
Daga nan sai ya jinjinawa JKS, bisa yadda ta zamo jigon samar da sauyi, da managarcin ci gaba. Garba Shehu ya ce cikin shekarun baya bayan nan, gwamnatin Najeriya mai ci karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta yi rawar gani a fannin bunkasa dangantaka da Sin.
Kaza lika Najeriya ta ci gajiya mai tarin yawa daga dangantakar moriyar juna tsakanin ta da Sin, ciki har da alheran da kasar ta samu daga zamanantar da layukan dogo, da fadada filayen jiragen sama, da gina tashoshin samar da wutar lantarki ta ruwa, da zamanantar da ayyukan gona. (Saminu Alhassan)