Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a wasu jihohi ciki har da Sakkwato da Legas da kuma Benuwe a watan Yuli, 2025.
NiMet ta bayyana hakan ne a wata sanarwar hasashen da ta fitar ranar Litinin, inda ta nuna jihohin da ke cikin haɗarin ambaliya sakamakon fara ruwan sama a fadin ƙasar.
- Ku Zama Cikin Shirin Samun Sauyin Yanayi – NiMet
- NiMet Ta Yi Hasashen Tsawa Da Ruwan Sama Na Tsawon Kwanaki A Arewa
Sauran jihohin da ke cikin haɗarin ambaliyar sun haɗa da: Kaduna da Zamfara da Yobe da Bauchi da Bayelsa da Jigawa da Adamawa, Taraba da Niger da Nasarawa da Ogun da Ondo da Delta da Edo da Cross River da Rivers da kuma Akwa Ibom.
NiMet ta bayar da shawarwari masu muhimmanci don rage illar ambaliyar, inda ta bukaci jama’a su tsaftace magudanan ruwa a gidajensu da unguwanninsu domin ruwa ya rika wucewa lafiya.
Hukumar ta kuma shawarci mutane da su guji tafiya ko tuki a cikin ruwa, domin ruwa na iya zama da hatsari ko kuma akwai barazana a ciki.
NiMet ta ce duk wanda ke zaune a wuraren da ruwa ke taruwa ko wuraren da aka bayyana yana da haɗari da su koma wuri mafi aminci.
An kuma shawarci jama’a da su tanadi kayan gaggawa kamar abinci mai yawa da ruwa da kayan taimakon gaggawa da fitila da na’urar adana lantarki ta ‘power bank’.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp