Hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) reshen Jihar Bayelsa ta samu amincewar shugaban hukumar na ƙasa, Isah Jere Idris wajen ƙaddamar da sintiri na musamman domin fatattakar baƙin haure a Jihar Bayelsa da aka yi wa laƙabi da “Saukar Shaho”.
An ƙaddamar da sintirin ne, saboda tsaftace jihar daga kwararowar baƙin haure da ke keta dokokin shige da fice da ƙungiyar ECOWAS ta tanadar wa mambobinta, wanda hakan ya sa dole a ƙarfafa tsaron rayukan ‘yan Nijeriya da dukiyoyinsu, sakamakon irin matsalolin tsaro da ake fuskanta wanda dole hukumomi da ke bakin iyakokin ƙasar nan su ɗauki matakan da suka kamata.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 9 ga watan Satumbar 2022 da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar NIS reshen Jihar Bayelsa ya rattaba wa hannu.
Sanarwar ta ce shirin ya samu amincewar Shugaban NIS, Isah Jere Idris da mai girma gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri domin ganin ya gudana kan kare haƙƙin baƙi da adalci da ‘yancinsu tare da fahimtar dangantakan da ke tsakanin yankuna na ƙasa da ƙasa wanda su ne za a yi la’akari da su wajen gudanar da sintirin.
A cewar sanarwar, ana tsammanin shirin zai gudana ne na tsawan mako guda da zai karaɗe ɗungu da saƙo da ke faɗin Jihar Bayelsa da dukkan ƙananan hukumominta.
Haka kuma ta ce wannan zai bayar da dama taskace duk wani bayanan baƙi da hana waɗanda ba ‘yan ƙasa su karya dokokin Nijeriya wajen ganin ba su jefa ƙuri’a a zaɓe mai zuwa ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa tun a gwajin farko a lamu na nuna cewa za a kawo ƙarshen karya dokokin shige da fice da tsaftace lamarin shige da fice tare da tabbatar da bin dokikin shige da fice wanda ya haɗa da bayar da izinin zama da sake sabunta takardun waɗanda aka ba su izinin zama a Jihar Bayelsa.