Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta shirya taron bita na kwanaki biyu ga jami’anta da ke aiki a sashin hulɗa da jama’a a faɗin ƙasar nan kan dabarun sadarwa game da yaƙi da shige da fice ba bisa ƙa’ida ba.
Taron bitar ya gudana ne tare da haɗin gwiwar gidauniyar ‘Konrad Adenauer Foundation’, wanda aka yi a otel ɗin Fraser Suites da ke Abuja, da ya samu halartar dukkan masu magana da yawun hukumar ta NIS.
Da yake gabatar da jawabi lokacin buɗe taron, shugaban NIS, CGI Isah Jere Idris ya bayyana farin cikinsa game da muhimmanci samun horo ga masu magana da yawun hukumar.
CGI Isah Jere, wanda ya samu wakilcin ACG AM Usman ya ce wannan bitar zai ƙara himma da ƙwazon jami’an wajen daƙile shige da fice ba bisa ƙa’ida ba, musamman ma fasa ƙwaurin shige da fice.
Shugaban hukumar ya yaba wa gidauniyar bisa wannan gagarumar ƙoƙari wajen inganta aikin hukumar. Yana mai cewar sakamakon bitar zai zama an samu ruɓanya harkokin sadarwar hukumar wajen faɗakar da al’umma kan yaƙi da dukkan ayyukan shige da fice waɗanda ba sa kan ƙa’ida a ɗaukacin iyakokin ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa hukumarsa ta ɗauki wasu dabaru wajen yaƙi da fasa ƙwaurin shige da fice waɗanda suke daidai da na Majalisar Ɗinkin Duniya kamar yadda dokar hukumar ta shekarar 2015 ta tanada.
A cewarsa, wannan bita ta zo a kan gaɓa domin za ta ƙara ƙoƙarin hukumar wajen ɗaukan matakai dangane da sha’anin harkokin shige da fice da ba sa kan tsari.
Ya buƙaci dukkan jami’an da suka amfana da shirin su yi ƙoƙarin yin amfani da abubuwan da suka koya daga wannan taron.
Tun da farko da yake jawabi, Daraktan Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Dakta Tony Luka Elumelu ya bayyana cewa taron bitar yana da matuƙar muhimmanci ga hukumar NIS.
Ya ce a matsayinsa na tsohon ma’aikacin hukumar NIS idan aka ambaci hukumar, dole yana da abubuwan faɗi game da ƙwazon shugabanni da jami’anta.
Daraktan ya ce idan ana buƙatar hukumar NIS ta isar wa ‘yan Nijeriya sahihin saƙo, to dole a ɗauki matakin horar da masu magana da da yawunta da ke faɗin ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa ta hanyar bai wa jami’an horo ne za a samu damar tace bayanai masu inganci ta yadda za a isar wa ‘yan Nijeriya. Ya ce bitar za ta taimaka wajen toshe ɓarna mai yawa, musamman harkokin shige da fice ba bisa ƙa’ida ba.
Ya nunar da cewa ta hanyar samun horo ne hukumar ta ciri tuta a tsakanin takwarorinta na ƙasar nan, musamman yadda ta sauya daga tsohon yayi ta koma na zamani inda hakan ya sauƙaƙa ayyukan hukumar.
Da yake zantawa da wakilin LEADERSHIP Hausa, ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da bitar wanda ya kasance mai magana da yawun hukumar NIS a Jihar Adamawa, Yawuba Muhammed ya bayyana cewa taron bitar zai ƙara bunƙasa harkokin ayyukan hukumar gaba ɗaya, musamman a iyakar Nijeriya da Kamaru. Kamar yadda ya ce, lallai wannan bita za ta taimaka wajen daƙile kwararowar baƙin haure a iyakan Nijeriya da Kamaru.
A cewarsa, ɗaya daga cikin muhummancin wannan bita shi ne, samun dabarun sadarwa domin sanar da cikakken sahihin rahoto ga mutane a zamanance.
Ita ma da take tofa albarkacin bakinta ga LEADERSHIP Hausa, jami’ar hulɗa da jama’a ta NIS a Jihar Bayelsa, ED Itimitula Ideinmo- Cokkey ta bayyana cewa bitar za ta ƙara musu himma wajen gabatar da bayanai, musamman kan yaƙi da shige da fice ba bisa ƙa’ida ba.
Ta ce kowanni jami’in hukumar yana da matuƙar muhimmanci ya samu irin wannan horo domin samun faɗakarwa mai inganci.
Gobe Talata ake sa ran kammala taron bitar jami’an na NIS a vangaren hulda da jama’a.