Kwanturola Janar na hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), Isa Jere Idris ya umarci kwanturolan hukumar reshen jihar Bayelsa, James Sunday da ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira tare da samar musu da tallafin ruwan sha domin tabbatar da suna shan ruwa mai tsafta kuma mai inganci ga yara da manya.
Umarnin kai tsaftacaccen ruwan shan ya shafi sansanin ‘yan gudun hijira ta OX- BOW da ke Lake inda gwamnatin jihar Bayelsa ta ajiye dubban ‘yan gudun hijira da iyalansu a wajen a matsayin wurin zama na wucin gadi.
A wata sanarwar da sashin yada labarai na NIS reshen Bayelsa ya fitar wa manema labarai ta nuna cewa, wannan karamcin na shugaban hukumar na zuwa ne sakamakon ambaliyar ruwan sama da aka samu wanda ya yi wa iyalai da gidaje daban-daban barna.
Kazalika, kwanturolan hukumar ya kuma mika sakon fatan alkairisa ga jami’ansa da ke aiki a Bayelsa da su ma ambaliyar ta shafa, kana ya umarci cewa kwamiti mai karfi daga shalkwatar hukumar ya ziyarci jami’ai su 64 da ambaliyar ta shafa tare da taya su alhini gami da shi shawarar abubuwan da suka dace.
Kwanturolan hukumar ta Immigration reshen jihar Bayelsa, James Sunday ya gode tare da yaba wa shugabansu bisa umarnin da ya bayar domin nuna tausayawa da jin kan wadanda lamarin ya shafa na ambaliyar ruwa.
James ya ce cikin taimakon Allah sun samu nasarar taskace muhimman takardu da bayanan hukumar kafin lokacin da ambaliyar ya zo ya yi barna a cikin shalkwatar hukumar da ke Bayelsa kuma yanzu haka ofishin hukumar na gudanar da aikace-aikacensa a sabon muhalli da ke kusa da Yenagoa kafin lokacin da za a gyara muhallin nasu domin su koma su cigaba da gudanar da aiki a ciki.
Har ila yau, sanarwar ta yi amfani da wannan damar wajen gargadin jami’an hukumar ta NIS da kada suke barin wajajen aikinsu a AWOL ko wani wajen domin kauce wa fushin hukumar da ka iya kaiwa a hukunta jami’i ko jami’a ko ma kora daga aiki gaba daya, “Za a ci gaba da sanya ido da bibiyar ayyukan jami’ai, duk ma’aikacin da aka samu da barin wajen aiki zai fuskanci hukunci,” in ji sanarwar.