Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), reshen Jihar Ribas ta gudanar da wani taron ƙara wa juna sani domin wayar da kai a kan ayyukan ‘yan ƙasashen waje a kamfanoni da kuma hulɗoɗin zuba jari a Birnin Fatakwal, babban birnin jihar.
Kwanturolan hukumar ta NIS na Jihar Ribas wanda har ila yau shi ne babban mai ilmantarwa a taron, CIS Sunday James, ya nemi kamfanoni da hukumomi kar su yi ƙasa a gwiwa a kan haƙƙoƙin da suka rataya a wuyansu na ɗaukar ‘yan ƙasa aiki waɗanda suka yi ilimi da kuma samun ƙwarewar aiki. A cewarsa, yin hakan ƙa;ida ce da ke cikin tsarin gudanar da ayyukan kamfanoni da aka bai wa lasisin ayyuka da ‘yan ƙasashen waje inda ake buƙatar kamfanonin su ɗauki ‘yan ƙasa da za su koyi aiki tare da maye gurbin ‘yan ƙasashen waje da zarar sun ƙware a fannonin da suke aikin a Nijeriya.
Har ila yau, a yayin gudanar da taron, an tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yadda ake keta dokokin shige da fice domin ilmantar da mahalartan daga kamfanoni da hukumomi abubuwan da suka kamata su riƙa gudanarwa tare da tabbatar da cewa suna biyan kuɗin ƙa’ida na ‘yan ƙasashen waje da ke aiki a ƙarƙashinsu duk wata, da irin bizar da ta kamata a riƙa amfani da ita da hanyoyin da suka kamata a bi wurin sallamar ma’aikaci, da yadda za a nemi wasiƙar da za ta wanke mutum daga zargin aikata mugun laifi da ta sa aka kores shi daga aiki kafin ya ajiye aiki ko sallamarsa da sauransu.
Wakazalika, an shawarci masu ɗaukar aiki su riƙa goge sunayen ‘yan ƙasar waje da suka sallama daga aiki daga cikin jerin waɗanda suke ƙarƙashin kulawarsu bayan sun bi duk matakai da ƙa’ida ta shimfiɗa domin waɗanda aka sallamar su iya samun damar yin aiki a wasu wuraren na daban.
Bugu da ƙari, an ilmantar da kamfanonin a kan bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa na sauya wa ‘yan ƙasashen waje sashen da suke aiki ko ɗaukar sabbi ta hanyar amfani da takardu da bizar da suka dace a koyaushe, domin kauce wa fushin doka kamar yadda aka tanadi hukunci a dokar shige da fice ta 2015 da ta 2017 da sauran dokoki na ƙasa da suka shafi hakan.
Kamar yadda Sunday James ya yi ƙarin haske, dokar ɓangaren zartarwa ta yi tanadin sauƙaƙa hada-hadar kasuwanci da ‘yan ƙasashen waje, wajen shigar da ‘yan ƙasa su ci gajiyar abin ta fuskar kimiyya da fasaha da ƙara buɗe hanyoyin samar wa matasan ƙasa ayyukan yi waɗanda suka yi karatu kuma suka samu tantancewar da ta dace daga wurin ƙwararru.
Ƙaramar Mataimakiyar Kwanturola Janar mai kula da Shiyya ta Biyar (Zone E) ta NIS wadda ta ƙunshi Jihohin Abiya, Akwa Ibom, Kuros Riba, Ebonyi, Imo da kuma Ribas wadda ta halarci taron a matsayin babbar baƙuwa, ta shawarci mahalarta taron daga kamfanoni da hukumomi su bi dokokin da aka shimfiɗa na aiki da ‘yan ƙasashen waje sau da ƙafa domin ci gaban ƙasa musamman ta fuskar bayar da bayanan wadanda suke aiki tare da su da kuma tabbatar da cewa suna yin abubuwan da suka dace.
Ɗaukacin mahalarta taron na NIS reshen Jihar Ribas daga kamfanoni da hukumomi sun bayar da gudunmawa a wurin taron ta hanyar neman ƙarin haske kan wasu abubuwa da suka shige musu duhu da kuma neman ƙarin bayani kan wasu kurakurai da ake cin karo da su saboda ajizanci na ɗan’adam wanda jami’an na NIS ke ganowa yayin da ɗan ƙasar waje ya zo shiga ƙasa, tare da jaddada buƙatar hukumar ta shige da fice ta riƙa aiki kafaɗa da kafaɗa da kamfanoni domin tabbatar da komai ya tafi daidai-wdaida yayin shiga ko fita ƙasa.