A yau Talata, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta buɗe katafaren babban ofishinta na Jihar Katsina tare da ƙaddamar da bayar da sabon ingantaccen fasfo na zamani a yankin.
Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya buɗe ofishin tare da shugaban hukumar ta NIS, CGI Idris Isah Jere a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar.
- TARON LEADERSHIP: Buhari Ya Sauya Fasalin Tsarin Tattalin Arzikin Nijeriya —Ministan Abuja
- Shugaban NIS Ya Sake Gargadin Marasa Gaskiya A Kan Harkokin Fasfo
Da yake jawabi a wurin, shugaban NIS, Isah Jere ya bayyana cewa, samar da sabon ingantaccen fasfo na zamani yana da matuƙar muhimmanci a cikin ayyukan da hukumar take yi wa ‘yan ƙasa, yana mai cewa, “tabbas muna sane da irin ƙalubalen da ‘yan ƙasa ke fuskanta wajen neman fasfo a lokutan baya, amma muna tabbatar muku da cewa bisa ƙoƙarin da muke yi daban-daban, kamar ƙaddamar da bayar da fasfo na zamani a Jihar Katsina, ba da jimawa ba waɗannan ƙalubalen za su kau. Muna ci gaba da ƙoƙarin buɗe ofisoshin karɓa da shigar da bayanan masu neman fasfo a jihar domin rage cunkoso. A kwanan nan za a kammala aikin ofishin na Daura tare da ƙaddamar da shi. Tuni aka samar da kayan aikin yin sabon fasfon a Katsina, nan da ‘yan kwanaki kaɗan komai zai yi daidai a fara gudanar da aiki, muna sa rai har da na Daura ma.”
Isah Jere ya bayyana cewa bisa ƙaddamar da bayar da sabon fasfon na zamani, haƙiƙa za a magance tafiyar hawainiyar da ake samu wajen neman fasfo, matuƙar dai mai nema ya bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa, ciki har da tabbatar da cewa ya gabatar da buƙatarsa ta shafin intanet tare da biyan kuɗi ta nan da kuma tabbatar da cewa bayanansa na fasfo sun yi daidai da na lambar shaidarsa ta ɗan ƙasa (NIN).
“Fasfo yana da matakai daban-daban, akwai mai aiki na tsawon shekara 10, wannan na waɗanda suka zama baligai ne da aka samar musu don magance yawan kai-komonsu a ofisoshin fasfo. Haka nan akwai sauran matakai wanda mai neman fasfo zai iya zaɓa.
“Sabon fasfon na zamani an yi shi ne da fasahar takardun zamani masu inganci wanda ruwa ba ya lalatawa, sannan yana da ƙarin alamomin tsaro guda 25 fiye da wanda ake bayarwa kafin ɓullo da shi (electronic passport). Shi wannan sabon da ake bayarwa shi ne ake yayi a halin yanzu a ɓangaren fasahar samar da fasfo a duniya, yana da ƙarko da kuma sauƙin amfani. Sannan zai yi matuƙar wahala a iya yin jabunsa saboda duk wanda ya yi yunƙurin haka ba wai kawai ba zai yiwu masa ba ne, a’a, da ya fara za a gano shi. Nijeriya ce ƙasa ta farko a duk faɗin Afirka da ta fara yin ƙaura zuwa sabon yayin na fasfo.” In ji Jere.
Shugaban na NIS, ya kuma ƙara da cewa, ana ci gaba da buɗe ofisoshin bayar da sabon fasfon, har ila yau ana ci gaba da bayar da tsohon shi ma har zuwa lokacin da za a mayar da kowace cibiyar fasfo ta zama mai bayar da sabon na zamani.
Haka nan ya yi nuni da cewa, buɗe sabon katafaren ofishin NIS na Jihar Katsina, ya sake tabbatar da irin duƙufar da hukumar ta yi wajen kula da jindaɗin jami’anta. A cewarsa, “wannan zai ƙara bunƙasa ƙwazonsu su ci gaba da yin aiki tuƙuru. Ina kuma kira tare da tunatar da cewa, bisa la’akari da yanayin tattalin arzikin ƙasa, ya zama wajibi mu kula sosai da abin da muke da shi tare da yin kyakkyawan amfani da wannan sabon ginin. Wajibi ne a kula da matakan riga-kafi a kowane lokaci.”
Ya gode wa Ministan cikin gida, Ogebeni Aregbesola bisa goyon bayan da yake bai wa NIS tun daga lokacin da aka naɗa shi minista. Haka nan ya yi godiya ga shugaban ƙasa bisa rattaba hannun amincewa a takardun hukumar waɗanda suka zamo silar samun nasarorin da ake gani.
Har ila yau, shugaban na NIS, CGIS Idris Isah Jere, ya yaba da irin haɗin kan da suke samu daga sauran abokan aiki na hukumomi daban-daban da ita kanta Gwamnatin Jihar Katsina, da sarakuna da sojoji da sauransu.
- https://leadership.ng/nis-redeploys-69-senior-officers/nigeria-immigration-service/