A wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa yaƙi da safarar baƙin haure, Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS) ta ƙaddamar da hukumar kula da asusun kula da ayyukan fasa ƙwaurin baƙin haure a hedikwatarta da ke Abuja.
ƙaddamarwar tana nuna wani gagarumin ci gaba a ƙudurin da NIS take da shi na ba wai kawai yaƙi da mutanen da ke yin safarar baƙin haure ba har ma da tabbatar da cewa waɗanda aka ceto daga masu safarar baƙin hauren an kula da su don ci gaba da rayuwarsu.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan ƙaddamar da hukumar, Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola wanda wani Darakta a ma’aikatar Cikin Gida, Mista Peter Obodo ya wakilta, ya yaba wa hukumar bisa kafa wannan asusun tare da yin kira ga mambobin kula da asusun su tashi tsaye wajen yaƙi da ayyukan masu fasa ƙwaurin baƙin haure.
Ya nunar da cewa daga yanzu, masu safarar baƙin haure ba za su ci gaba da cin karensu ba babbaka ba kamar yadda suka saba.
Tun da farko a nasa jawabin, Shugaban NIS, CGI Isah Jere Idris wanda shi ne shugaban hukumar kula da asusun, ya bayyana cewa ‘ayyukan masu safarar baƙin haure sun ɗauki wani sabon salo da ba za a taɓa amincewa da su ba, don haka ya kamata a yi duk mai yiwuwa wajen ganin an magance.
“Taron da muke yi a yau yana ɗaya daga cikin irin ƙoƙarin da muke yi na ganin mun yi wani ƙwaƙƙwaran bayani game da shirye-shiryen da muke yi na ganin masu fasa ƙwaurin baƙin haure sun kwashi kashinsu a hannu.” In ji shi.
Ya sake nanata cewa aikin hukumar asusun yana da tsauri kuma da girma don haka yana buƙatar dogon lokaci, jajircewa da gogewa daga membobin don samun nasara mai kyau a yaƙi da safarar baƙin haure.
Sashe na 97 na Dokar Shige da Fice ta 2015 ya tanadi kafa Asusun Tallafa Wa Baƙin Haure wanda zai riƙa samun kuɗaɗen gudanarwa daga duk abin da aka samu na dukiya da sayar da kadarorin masu safarar baƙin hauren bisa sahalewar kotu.
Har ila yau, ya tanadi cewa Hukumar Gudanarwa na Asusun za ta ƙunshi wakilai daga: Ma’aikatar Cikin Gida; Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice (NIS) a matsayin shugaba; Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya; Ma’aikatar Kudi ta Tarayya; Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma ta Tarayya da Ofishin Akanta-Janar.
Sauran sun haɗa da: Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗi; Babban Bankin Nijeriya; da kuma Hukumar Hana Fataucin Bil’adama ta ƙasa (NAPTIP) da sauransu.
Cikin manyan abubuwan da aka gudanar a taron akwai ƙaddamar da wakilan asusun daga ma’aikatu da hukumomin da suka haɗa da: Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, da ta Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a, da NAPTIP, da Ofishin Akanta-Janar da sauran wadanda Mista Peter Obodo mai wakiltar ma’aikatar cikin gida ya gabatar.
Ƙaddamar da Hukumar Gudanarwar Asusun dai, na nuna an sake ayyana yaƙi da masu safarar baƙin haure da haramtattun kadarorinsu cikin sabon salo da zai zama mai alfanu a bisa jagorancin shugaban hukumar ta NIS, CGI Isah Jere Idris.