A wani sabon yunkuri na da Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta bullo da shi a Jihar Ribas don tattara bayanan ‘yan ci-rani.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwanturolan jihar, James Sunday, ya fitar inda ya ce dole ne jami’an hukumar su yi aiki don tattara bayanan sirri.
- Jami’an Tsaro Sun Tsare Peter Obi A Birtaniya
- ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 2 Kan Zargin Jefe Wani Direba Har Lahira A Ondo
A cewarsa jami’an hukumar za su yi aiki don gano kurakurai da ake tafkawa tare da bankado su don cafke wadanda suke hannu.
Kazalika, ya ce hukumar za ta sanya ido zaman wadanda ba ‘yan Nijeriya ba da alakarsu ta aiki da kamfanoni wanda ya yi daidai da dokar hukumar ta 2015.
Ya ce hukumar ta fara samun sakamako mai kyau bayan ziyartar wuraren da ake zargin ‘yan ci-rani ke karya dokoki tare da kama su.
Sunday, ya ce wannan na daga cikin tsarin sabbin ayyuka da shugaban hukumar na kasa, Idris Isah Jere ya bullo da su din ingata ayyukanta da kuma tsare iyakokin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp