Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa ta mika wasu mutane 11 da aka yi fataucin su zuwa kasar Libiya ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) reshen Jihar Sokoto.
Kwanturolan hukumar shige da fice da ke iyakar Illela, Ado Rano Sabo, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a 10 ga watan Maris, 2023 lokacin da yake mika wadanda abin ya shafa ga hukumar ta NAPTIP a Sokoto.
- Sabon Kwanturolan NIS A Ribas Ya Gargadi Jami’ansa Kan Bin Dokokin Aiki A Zaben 2023
- Shugaban NIS Ya Kaddamar Da Ofishin Fasfo Na Zamani A Zariya
Rano, ya ce, mutane 11 dukkansu mata ne, an kama su ne a Jamhuriyar Nijar a kan hanyarsu ta zuwa kasar Libiya.
Jami’an ‘yan sandan jamhuriyar Nijar ne suka dawo da su gida Nijeriya tare da mika su ga hukumar kula da shige da fice ta kasa da ke kula da kan iyaka ta Illela.
Kwanturolan hukumar, Ado ya kara da cewa, ‘yan matan sun fito ne daga sassa daban-daban na kasar nan kuma yawancinsu suna da shekaru tsakanin 19 zuwa 37.
Rani, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su daina gudanar da irin wadannan tafiye-tafiye masu hatsarin gaske, inda ya ce galibin wadanda abin ya shafa ana amfani da su wajen yin aikin kwadago, karuwanci da sauran abubuwan da ba su kamata ba.