Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS), ta karrama wasu zaƙaƙuran jami’anta sama da 40 da suka nuna bajinta a fagen aiki, a wata liyafar abincin dare ta ƙarshen shekarar 2022, da ta saba shiryawa a duk shekara.
An karrama jami’an ne a yayin liyafar da ta gudana a shalkwatar hukumar ranar Juma’ar nan.
Da yake jawabi a bikin, Kwanturola Janar na NIS, Isah Jere Idris ya bayyana cewa an karrama jami’an ne bisa cancanta inda ya yi kira gare su, su ruɓanya ƙwazonsu domin saka wannan karamci da aka yi musu kana ya hori waɗanda ba su samu ba su ƙara himma domin ganin sun shiga cikin waɗanda suka cancanta a baɗi idan Allah ya kai mu.
Har ila yau, ya ce, baya ga waɗanda aka karrama akwai kuma waɗanda aka hukunta daban-daban bisa samun su da hannu a laifukan da suka shafi zamba ta ɗaukar aiki da sauransu. “An kori jami’ai 8, an hukunta 18, sannan akwai wasu da ake kan bincike a kansu.” In ji shi.
Da yake tsokaci kan nasarorin da hukumar ta samu a 2022, CGI Isah Jere ya ce an samu ƙarin cibiyoyin fasfo da aka mayar da su tsarin sabon fasfo da aka inganta a zamanance, a ciki da wajen ƙasar nan, kana ya ba da tabbacin ci gaba da yin haka har a kai ga mayar da ɗaukacin cibiyoyin fasfo a ƙarƙashin sabon tsarin.
Dangane da batun kyautata walwalar jami’ai kuwa, Isah Jere ya bayyana cewa akwai manyan jami’ai guda 5 da aka ƙara musu girma zuwa matsayin manyan mataimakan Kwanturola Janar, sannan ya ce zai yi tsayin daka wajen ganin an fitar da sakamakon jarrabawar ƙarin girma da aka yi wa sauran jami’ai domin a samu ƙarin waɗanda za a ciyar da su gaba.
Wakazalika, CGI Isah Jere ya bayyana cewa a ɓangaren tsaron iyaloki, sun ɗauki ƙarin matakai daban-daban, yana mai cewar, “Mun ziyarci NIMASA mun tattauna a kan ƙarfafa tsaron iyaka, yanzu haka da nake magana da ku an kammala yarjejeniyar da za mu rattaba hannu da su. Haka nan ba da jimawa ba, muka yaye wasu dakaru mata 61 da za mu tura su aikin tsaron iyalokin ƙasa baya ga sauran matakai na aiki da na’urorin zamani da muke ci gaba da ɗaukawa don tabbatar da tsaron iyaka.”
Isah Jere ya sa an yi tsit na minti ɗaya domin girmamawa ga jaruman dakarun NIS da suka rasa rayukansu a bakin aiki wajen tabbatar da tsaron iyaka.
Har ila yau, ya yi bayanin cewa
Ya ƙaddamar da shirin samar da gidaje kuma ba da jimawa ba za a fara rabawa ta hanyar ƙungiyar gama kai ta jami’an NIS domin ƙara kyautata jin daɗin jami’ai.
Ya gode wa Shugaba Buhari bisa goyon bayan da yake bai wa NIS na tsawon lokaci. Haka nan ya gode wa Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola da babban sakataren ma’aikatar tare da dukkan mambobin hukumar gudanarwar ma’aikatar bisa tallafa wa samun nasarorin hukumar.
A nashi ɓangaren, wakilin ministan cikin gida, Janar Bassey mai ritaya, ya bayyana cewa, tun lokacin da aka naɗa shi a matsayin kwamuishina a hukumar gudanarwar ma’aikatar cikin gida, NIS ce kawai take shirya irin wannan biki, kana ya yi kira ga sauran takwarorinta su yi koyi.
Ya yaba wa CGI Isah Jere Idris bisa ƙoƙarin kawo sauyi da yake yi tun lokacin da ya karɓi ragama, inda ya buƙace shi ya ci gaba da hakan.
Ya ce minista yana taya ɗaukacin ‘Yan Nijeriya murnar bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara ta 2023.
Shi kuwa DCG Haliru wanda ya yi jawabin godiya, ya yi kira ga waɗanda suka samu lambobin yabon kar su ɗauki lamarin a matsayin abin da za su shantake, amma su ƙara himma da ƙwazo.
Haka nan ya yi kiran haɗin gwiwa a tsakanin rundunonin tsaro domin samun ƙarin nasara a kan sha’anin tsaron ƙasa.
Haliru ya ƙara da cewa, a zamanin shugabancin CGI Jere sun samu lambobin yabo guda 5, wanda ba a taɓa bai wa wani mai muƙamin DCG Lambar Yabo ta ƙasa (MFR) ba sai a zamaninsa.
Ya nemi jami’ai su yafe wa juna idan akwai laifi a tsakaninsu, kana su ƙara haɗin kai domin aiki ya tafi daidai wa daida.
ɗaya daga cikin waɗanda aka bai wa lambar yabon, ya yi godiya ga NIS a madadin saura, “da ta ga cewa mun dace ta karrama mu, kuma muna ƙara jaddada cewa za mu ƙara zage damtse mu ci gaba da aiki tuƙuru.”