Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta Kasa (NIS) ta yi kawance da takwararta ta duniya (IOM), da Hukumar Yaki Da Safarar Bil’adama (NAPTIP) da Sashen Ayyyukan Lafiya na PHS, wajen shirya wani taron kara wa juna sani da nufin samar da horo da dabarun aiki ga jami’anta.
An shirya horaswar ce a karkashin shirin da aka yi wa sunan TSI a takaice.
A wata sanarwa da Jami’in hulda da jama’a na NIS, Amos Okpu ya fitar, NIS ta bayyana cewa shirin yana samun tallafin hukumar kula da shige da fice ta duniya (IOM) da nufin bunkasa ayyuka a iyakokin kasa da kara sanya ido kan harkokin shige da fice a Nijeriya tare da taimaka wa hukumomin kula da shige da fice.
Shirin na da manufar bunkasa kwazo da hazakar jami’an da ke aiki a hukumomin dakile safarar mutane da shige da fice ta barauniyar hanya domin ayyuka su rika tafiya yadda ya dace a kowane lokaci.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin karo na na biyu, Shugaban Hukumar ta NIS, Isah Jere Idris, wanda ya samu wakilcin mataimakin kwanturola Janar mai kula da harkokin biza, Ishaka Abdulmumini Haliru, ya misalta kokarin abokan hukumar wajen kara bunkasa kwazon aikin jami’an NIS da NAPTIP a matsayin wani gagarumin ci gaba da zai kyautata harkokin shige da fice da dakile yawan safarar mutane ta barauniyar hanya, yana mai cewa hakan zai kara kyautata alaka a tsakanin bangarorin.
Ya ce, a kowani lokaci suna kula sosai da ba da fifiko ga sashin horar da jami’ansu domin tabbatar da ayyuka na gudana yadda ya dace, kan haka ne ma ya nuna farin cikinsa da wannan shirin.
A nata jawabin, darakta-janar ta Hukumar NAPTIP, Dakta Fatima Waziri-Azir, ta ce, IOM na tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta kwazon jami’ai a fagen aiki a-kai-a-kai.
Ta yi kira ga hukumomi da jami’an da abin ya shafa da su yi amfani da wannan damar tallafin da suke samu daga kungiyoyin kasashen waje wajen inganta ayyukansu a kowani lokaci.
Sannan, ta bukaci jami’an NIS da NAPTIP da su ci gaba da kyautata alakar aiki mai inganci a tsakaninsu domin hada karfi da karfe waje guda don yaki da safarar mutane da jigila ta kai-komo ta barauniyar hanya.
Shi kuma a bangarensa, daraktan ayyukan lafiya na PHS, Dakta Geoffrey Okatubo, ya ce a ‘yan kwanakin baya sashen kula da lafiya ya fuskanci barazanar annobar korona da aka fuskanta, a yanzu kuma ga cutar kyandar biri (Monkey pox) da ake fama da ita a halin yanzu.
Sai ya nuna kwarin guiwarsa na cewa da hadin guiwar abokan aiki na cikin kasar Nijeriya da kasashen waje ana samun sakamako mai kyau wajen kula da lafiya.
Shugaban NIS, Isah Idris Jere ya sha nanata cewa zai mayar da hankali ga horas da jami’a domin inganta ayyukan hukumar a kowane sashe.