Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) karkashin jagorancin Kwanturola Janar Wuraola Adepoju ta daukaka darajar jami’anta kusan 7000 a fadin hukumar.
Karin girma na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren hukumar, Alhaji Jafaru Ahmed.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mukaddashin ma’aikatar, Mista Kenneth Kure, wanda shi ma ya samu matsayin Mataimakin Kwanturola, yawan jami’an da aka kara girma ya hada da manyan jami’an da suka zana jarrabawa da kuma kananan ma’aikatan da aka kara wa girma bisa sakamakon cancanta.
A wani labarin kuma, Babban Kwanturola Janar, Wuraola Adepoju ya amince da nadin tsohon kakakin hukumar, Tony Akuneme a matsayin Kwanturola na babban birnin tarayya Abuja, yayin da Kwanturola Joseph Dada ya zama sabon babban kwanturola Janar.
Mista Dada, wanda ya kammala karatunsa a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile Ife, ya yi aiki daban-daban a hukumar ta NIS, kuma har zuwa lokacin da aka kara masa girma, Kwanturolan da ke kula da harkokin jiragen ruwa a hedikwatar hukumar.
Idan ba a manta ba kwanan nan ne aka sake tura Kwanturola 12 zuwa jihohi daban-daban da suka hada da birnin tarayya, Kano, Jigawa, Ondo, Ogun da dai sauransu.
A jawabinta ga Jami’ai da Ma’aikatan Hukumar a lokacin faretin wata-wata, hukumar ta bukaci da su fifita martabar aikin fiye da bukatun kashin kansu domin NIS na daya daga cikin manyan hukumomin da alhakin kare dukiyoyin al’umma ya rataya a wuyansu.
Ta yi alkawarin ba da fifikon jin dadin ma’aikata, ta kuma sha alwashin cewa daga yanzu dole ne a yi wa manyan jami’ai karin girma domin abin takaici ne ganin yadda wasu tsofaffin jami’ai suka dade a mataki daya.
“Duk ma’aikacin da ba shi da kwarin gwiwa ba zai iya ba da tabbacin aiki mai ingancin ba,” in ji Misis Adepoju.