Kungiyar Kwadago na neman a biya ma’aikatan Nijeriya Naira Miliyan daya a matsayin sabon mafi karancin albashi, in ji shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero.
Ajaero ya bayar da hujjar wannan matsayar ne saboda hauhawar farashin kayayyaki da kuma wahalhalun da ma’aikatan Nijeriya ke fuskanta a baya-bayan nan sakamakon cire tallafin man fetur.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wasu Mutum 4 A Kauyen Nkienzha Na Jihar Filato
- An Kammala Gasar Tseren Dawakai Ta Ƙasa-da-ƙasa A Jihar Kano
Idan an amince da kudurin, ana sa ran za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin a watan Afrilun 2024.
Tuni dai gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai duba mafi karancin albashi daga Naira 30,000 da ake biya a duk wata.
Amma, Ajaero, wanda ya yi magana a gidan talabijin na Arise News a ranar Litinin, ya ce sabuwar bukatar ita ma ta biyo bayan tsadar rayuwa ne a karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu, wacce ta aiwatar da tsare-tsaren da suka haddasa hauhawar farashin kayayyaki kamar cire tallafin man fetur.
“Za ku iya tuna cewa, a lokacin da muke tunanin Naira 200,000 (a matsayin mafi karancin albashi) farashin canji ya kai kusan Naira 800 ko 900 akan dala daya, amma a yanzun, farashin canji ya kai kusan Naira 1,400 ko ma fiye da haka akan kowacce dala daya” inji Ajaero.