Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni huɗu don warware duk matsalolin da ke tsakaninta da ƙungiyoyin jami’o’i da na kwalejojin fasaha, idan ba haka ba za ta jagoranci yajin aiki na ƙasa baki ɗaya.
Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ya ce ƙungiyar za ta tallafa wa ƙungiyoyin don tabbatar da cewa gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma tare da inganta albashi da kuɗin gudanarwa a cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare.
- Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu
- Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu
Ya gargaɗi gwamnati da kada ta sake tura wakilai zuwa taruka ba tare da ikon yanke shawara ba, yana mai cewa hakan yana ƙara tsananta rikicin da ake fama da shi.
Ajaero ya kuma bayyana cewa NLC yanzu za ta bi tsarin “Ba a biya, babu aiki” a matsayin martani da gwamnati ta yi amfani da shi a kan ASUU.
Ya ce yawancin matsalolin sun shafi albashin baya, alawus da aka dakatar, da kuma rashin isasshen kuɗin gyaran makarantu.
NLC ta kuma buƙaci gwamnati ta bi shawarar UNESCO wacce ta ke cewa ya kamata a ware aƙalla kashi 25 cikin 100 na kasafin kuɗi na kowace shekara ga ilimi.
Ajaero, ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin makonni huɗu, NLC za ta haɗa dukkanin ma’aikata na ƙasa don gudanar da yajin aiki na ƙasa baki ɗaya.