Lauyoyi na kungiyar kwadago ta Nijeriya, NLC da shugabanta, Kwamared Joe Ajaero, sun bukaci a dage zaman tuhuma da rundunar ‘yansandan Nijeriya ta yi masa kan wasu zarge-zarge.
A wata wasika da NLC karkashin jagorancin Samuel Ogala ta aikewa babban sifita na ‘yansanda, da kuma mataimakin kwamishinan ‘yansanda (DCP) Mohammed Ahmed Sanusi, a ranar Talata, ta bayyana cewa, gajeriyar sanarwar gayyatar, ba zai yi wu a girmama gayyatar ba a ranar da aka tsara.
- Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Afrika Ta Kai Wani Sabon Matsayi
- Gwamnatin Sokoto Za Ta Sayar da Tireloli 300 Na Shinkafa A Farashi Mai Rahusa
A martaninsa, Ajaero, ta hannun lauyoyinsa, ya bayyana aniyarsa na yin biyayya ga bukatar ‘yansandan, amma ya ce, yana bukata a mayar da gayyatar zuwa ranar 29 ga watan Agusta, 2024.
Wasikar ta kuma bukaci cikakken bayani kan yanayin zargin da ake yi wa Ajaero, wadanda suka hada da hada baki, daukar nauyin ta’addanci, da cin amanar kasa, da zagon kasa, da kuma laifuffukan kutse ta yanar gizo.
Bugu da kari, kungiyar NLC, a ranar Talata, ta yi gargadin yiwuwar daukar matakin da ya dace na afkawa zanga-zanga a fadin kasar idan rundunar ‘yansandan Nijeriya ta tsare shugabanta, Kwamared Joe Ajaero.
An cimma wannan matsayar ne bayan wani taron gaggawa na majalisar zartarwa ta kungiyar da aka gudanar a ranar Talata, inda majalisar ta bayyana matakin da ‘yansandan suka dauka a matsayin “binciken da ba shi da tushe sai dai zallar siyasa”