Shugaban masu fafutukar kafa Kasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya maka gwamnatin tarayya a gaban kotun koli, inda ya roke ta da ta yi watsi da karar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan hukuncin kotun daukaka kara da ta sallame shi daga hannun jami’an tsaron farin kaya (DSS).
Idan dai ba a manta ba a ranar 23 ga watan Oktoba ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar a madadin Kanu, inda ta kalubalanci ikon babbar kotun tarayya da ta yi watsi da tuhumar da ake masa.
- Bindigogi 10 Mafiya Tsada A Duniya
- Yadda Qatar Ta Zo Da Sabon Salo Na Ba-zata A Gasar Cin Kofin Duniya
Alkalan Kotun Daukaka Kara a cikin hukuncin da suka yanke a cikin daukaka kara mai lamba: CA/ABJ/CR/625/2022; TSAKANIN: MAZI NNAMDI KANU DA GWAMNATIN TARAYYAR NIGERIA, sun amince da daukaka kara, inda aka yi watsi da tuhume-tuhume bakwai da kotun sauraren kararrakin ta yi masa.
Gwamnatin tarayya ta kai karar kotun daukaka kara kan bukatar dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke, duk a kokarinta na ci gaba da tsare Kanu.
A ranar 28 ga watan Oktoba ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke a ranar 13 ga watan Oktoba.
Tawagar lauyoyin Kanu sun shigar da kara a gaban kotun koli inda suke neman kotun koli ta shiga tsakani domin a yi watsi da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin na shugaban kungiyar IPOB.
Sun kuma kai kara zuwa kotun koli domin tantance batutuwan da suka shafi hukuncin kotun daukaka karar.