Kamfanin Dangote ya musanta rahotannin da ke cewa Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), ya fara sayen man fetur daga matatarsa a kan Naira 897 kan kowacee lita.
Babban Jami’in Hulda da Jama’a na Kamfanin, Anthony Chiejina, ya ce matatar Dangote ba za ta iya kayyade farashin man fetur ba har sai sun kammala kulla yarjejeniya da NNPCL.
- NCoS Ta Musanta Zargin Rashin Bai Wa Fursunoni Isasshen Abinci A Kano
- Farashin Kayayyaki Zai Sake Tashi A Nijeriya – MAN
Ya bayyana cewa NNPCL bai fara dakon man fetur daga matatarsu ba, don haka batun farashi bai taso ba.
Kamfanin Dangote ya bayyana cewa farashin man fetur yana karkashin ikon gwamnati, kuma ba su da iko wajen yanke ko sauya farashin.
Sun bukaci jama’a da su yi watsi da rahotannin game da farashin man fetur, yayin da suka tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa suna yin adalci a harkokinsu.
Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana aiki kan fitar da sabon farashin man fetur.
Matatar Dangote, wadda za ta ke samar da gangar man fetur 650,000 a kullum, ta fara samar da man fetur kuma ta ce nan ba da jimawa ba gidajen mai za su fara samu.