Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL), ya sake kara farashin litar man fetur, Naira 1,020 a Jihar Legss, yayin da a Babban Birnin Tarayya, Abuja ake sayar da litar kan Naira 1,050.
Wannan sabon karin na zuwa ne mako uku da karin da kamfanin NNPCL ya yi.
- Sin Ta Yi Kira Da a Yi Hakuri Da Juna Tare Da Nuna Adawa Da Keta Zaman Lafiya a Yankin Gabas Ta Tsakiya
- Gwamna Abba Ya Amince Da Sabon Mafi Karancin Albashi Na ₦71,000 Ga Ma’aikatan Kano
A ranar 9 ga watan Oktoba 2024 ne kamfanin ya kara farashin litar zuwa Naira 1,030 a Abuja, sai kuma farashin ya tashi a Jihar Legas daga 897 zuwa Naira 998.
Rahotann daga gidajen man NNPC sun tabbatar da cewa a Legas farashin yana kai wa har 1,025 kan kowace lita.
Karin farashin na zuwa yayin da ‘yan Nijeriya suka fara rage amfani da mai saboda tsadar da ya yi tare da samun raguwar ababen hawa a kan tituna.
Wasu alkaluma sun nuna cewar ‘yan Nijeriya sun rage amfani da litar, wanda daga lita miliyan 60 a kowace rana ya dawo zuwa lita miliyan 4.5 a watan Agustan 2024.