Kamfanin man fetur na kasa (NNPC), ya bayyana rahotan ayyukansa na shekarar 2023, wanda ya nuna cewar ya samu ribar Naira triliyan 3.3.Â
Babban mai kula da harkokin kudaden kamfanin, Umar Aliyu, ya ce an samu karin abin da ya kai Naira biliyan 700 a kan ribar da ya samu a 2022, wanda shi ne kashi 28 na kudaden da suka samu.
- Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Karuwar Zargin Cin Zarafi A Rundunar Sojojin Amurka
- Bayan Sauke Arabi, Tinubu Ya NaÉ—a Usman A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar NAHCONÂ
Ya ce sun samu nasarar ne sakamakon jajircewar su wajen inganta ayyukan da suke yi duk da tarin matsaloli da suke fuskanta.
Ya danganta ci gaban da suka samu da sabuwar dokar mai ta kasa wadda ta mayar da kamfanin ya zama na kasuwanci mai dauke da hannayen jarin hukuma da kuma jama’a.
Aliyu, ya ce nan gaba kadan za su bayyana shirin sayar da hannayen jarinsu da zarar an gudanar da taron wadanda ke rike da jarin kamfanin da kuma hukumar gudanarwarsa.
Har wa yau, ya kuma bayyana aniyarsu ta ganin sun kara yawan man da Nijeriya ta ke hakowa kowace rana zuwa ganga miliyan biyu nan da karshen 2024.
Dangane da dogon layukan man da ake ganin a birnin Legas da Abuja, mataimakin shugaban da ke kula da bangaren mai, Dapo Segun, ya ce suna hada kai da masu ruwa da tsaki domin ganin an warware matsalar.