Hukumar kula da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ta ce, za a kammala aikin gyaran matatar man fetur ta Kaduna (KRPC) a karshen shekarar 2024 bayan shafe shekaru a rufe saboda rashin kulawa.
Babban mai kula da matatar KRPC, Mustafa Sugungun ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a yayin ziyarar sa ido a matatar man da kwamitin ‘yan majalisar dattijai a karkashin jagorancin Sanata Ifeanyi Ubah suka kai matatar.
- Hukumar NCAA Ta Karyata Rahoton Sayen Mota Ta Fiye Da Naira Miliyan 250
- Gwamnati Na Buƙatar Dala Biliyan 10 Don Farfaɗo Da Ɓangaren Wutar Lantarki
Ya bayyana cewa, matatar mai tace ganga 110,000 a kowace rana za ta fara aiki da kashi 60 cikin 100 nan da karshen shekara, yayin da ake sa ran za ta ci gaba zuwa kashi 100 na cikakken aiki daga baya.
Shugaban na KRPC ya bayyana cewa, aikin gyaran, wanda a halin yanzu ya kai kashi 40 cikin dari, ana sa ran kammala shi cikin wa’adin da aka kayyade.