Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta musanta rahotannin da kafafen yada labarai suka yada game da siyan mota kirar Toyota Landcruiser ta shekarar 2022 da kudinta ya haura Naira Miliyan 250.
NCAA ta kuma yi barazanar gurfanar da mawallafin jaridar a gaban kotu matukar bai goge labarin karyar ba.
- JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar 2024, Sakamako 64,624 Na Karkashin Bincike
- Gwamna Obaseki Ya Amince Da Biyan Naira 70,000 Sabon Mafi Ƙarancin Albashi
In ba a manta ba, a karshen makon da ya gabata ne wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta rahoto cewa “watanni kadan bayan nadin mukaddashin babban darakta na hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Nijeriya, NCAA, Kyaftin Chris Najomo, ya yi almubazzaranci da dukiyar gwamnati tare da cin zarafin ofishinsa.”
Sai dai da yake mayar da martani ga rahoton, daraktan hulda da jama’a na NCAA, Mista Michael Achimugu, ya ce, babu inda hukumar NCAA ta biya kudin mota tun bayan zuwan Najomo a matsayin shugaban hukumar.