• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NNPP Na Zargin Kwankwaso Da Hannu Wajen Nasarar Gawuna Da Kwace Zaben Kano A Kotu

by Muhammad
2 years ago
Kwankwaso

Jam’iyyar NNPP ta zargi tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso, da hannu kan rashin nasarar da gwamnan Kano, Yusuf Abba, ya samu a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar.

Jam’iyyar ta ce Kwankwaso ya sayar da NNPP ga jam’iyya mai mulki ta APC kan tattaunawarsa a batun kujerar minista da ya yi zawarci a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

  • Jam’iyyar NNPP Ta Dakatar Da Kwankwaso Na Wata 6 Kan Mata Zagon Kasa
  • DA DUMI DUMINSA: Kotu Ta Dakatar Da Korar Kwankwaso Daga Jam’iyyar NNPP

A ranar Laraba ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta kori Abba tare da bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kotun mai alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a, Oluyemi Akintan-Osadebay, ta janye takardar shaidar cin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta bai wa Abba Yusuf.

Da ake bayyana dalilan da suka sa aka tsige gwamnan Kano, kotun ta ce ratar kuri’un da jam’iyyar NNPP ta samu ta samu ne ta haramtacciyar hanya ba ta hanyar da ta dace ba, kuma hanyar da ta bi wajen samun kuri’un basu dace da dokar zabe ta 2022 ba.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

Alkalan sun cire kuri’u 165,663 daga jam’iyyar NNPP, inda suka kara da cewa a jikin kuri’un guda 165,663 babu sa hannun jami’in zabe da satamfi da kwanan wata kamar yadda doka ta tanada, don haka suka bayyana cewa kuri’un ba su da inganci.

Da yake mayar da martani, daya daga cikin jagororin jam’iyyar NNPP a yankin Kudu maso Yamma, Alhaji Abass Akande Onilewura, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis, ya ce rashi da jam’iyyar ta yi a Kano ya tabbatar da zargin kin jinin jam’iyyar da aka yi saboda Kwankwaso.

Onilewura ya jaddada cewa tsohon dan takarar jam’iyyar NNPP na da hannu dumu-dumu da hadin baki da Jam’iyyar APC wanda hakan ya haifar da babban rashi da jam’iyyar ke fuskanta kotunan zabe a Kano.

Ya nanata cewa Kwankwaso bai bi ka’ida ba wajen zabar wasu daga cikin ‘yan takara a jam’iyyar, lamarin da ya ce ya kai shigar da Jam’iyyar cikin halin da ta samu kanta a yanzu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure
Manyan Labarai

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai
Manyan Labarai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86
Da ɗumi-ɗuminsa

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Next Post
Annabi

Sabon Karatu: Tsantseni Da Gudun Duniya Na Annabi (SAW)

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.