Jam’iyyar NNPP ta kaddamar da kwamitin sulhu da zaman lafiya na bayan kammala zaben fid da gwani na ‘yan takarkara a Jihar Neja, domin tafiya tare wajen samun nasarar babban zabe mai zuwa.
Da yake karin haske ga manema labarai, shugaban jam’iyyar na jiha, Hon. Mamman Garba Damisa, ya ce sun kafa kwamitin mutane bakwai domin samun hadin kai da kuma mara wa jam’iyyar NNPP baya wajen samun nasarar babban zabe mai zuwa.
A cewarsa, an yi zaben fid da gwani kuma an kammala kowani dan jam’iyya na da muhimmanci, wanda ya samu nasarar zaben fid da gwani da wanda ya fadi, saboda babban aikin kwamitin shi ne hada kan ‘ya’yan jam’iyya wajen yin aiki tare ta hanyar janyo wadanda suka fadi a zaben fid da gwani a jika, musamman ganin suna da bukatar kawo canji da samun nasarar zabe mai zuwa.
‘Yan kwamitin da suka hada da Janar Abubakar Imam, a matsayin shugaba, sai tsohon kwamishina kuma jagoran Kwankwasiyya a Jihar Neja, Hon. Danladi Umar Abdulhamid (Tambarin Kagara) mai shiga tsakani, Saura sun hada da Hon. Mohammed Bashir Abacha, Kwamaret Garba Mohammed, Kwabo, da Misis Mariam Remi Maku, sai Injiniya Abubakar Abdullahi Gwada a matsayin mamba, Hon. Garba S. Malami shi ne sakataren kwamitin.
Jam’iyyar ta samu mutane uku ne da suka yi takarar gwamnan jihar, wanda a cewar shugaban jam’iyyar dukkansu sun yi korafi har dan takarar da ya samu nasarar zama dan takarar kujerar gwamna, dan haka wannan kwamitin zai saurari korafe-korafen jama’a tun daga kan ‘yan takara har kan ‘ya’yan jam’iyya domin warware duk wata rashin jituwa a cikin jam’iyya.