Jam’iyyar NNPP, ta nemi kasashen Amurka, Tarayyar Turai (EU) da Tarayyar Afirka (AU) su shiga tsakani kan shari’ar gwamnan Kano, inda ta danganta shari’ar a matsayin magudin hukuncin kotu domin kwace nasarar da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya samu.
A zanga-zangar da aka gudanar a ranar Laraba a ofisoshin jakadancin Amurka, Tarayyar turai da tarayyar kasashen Afirka a Abuja, mukaddashin shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Abba Kawu Ali, ya ce, Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben jihar ta yanke, don haka, kotun ta nuna cewa, gwamna Yusuf ne ya lashe zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
Ya kara da cewa, manufar zanga-zangar da jam’iyyar NNPP ta gudanar a ofisoshin jakadancin, ita ce ta sanar da dukkanin kasashe da kungiyoyi masu kishin Dimokuradiyy halin da kotunan zabe ke ciki a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp