Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta sanar da cewa, ta sauya bin ka’idar shigar manya motoci shiga cikin Tashar, inda ta bayyana cewa, gabatar da gudanrin shedar lambar motocin da kuma takardar shedar da ake mannawa a jikin mocin ta tabatar da bayat da da kariya a kofar shiga Tashar wato MSS, Hukumar, ba za ta aminta da ita ba.
Kamfanin da ke kula da barin yin zirga-zirgar manyan motocin a cikin Tashar wanda ya yi hadaka da sashen rage cunkoson manyan motocin na Hukumar ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya fitar.
- Ba Mu Amince Da Yi Wa Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Shari’a A Sirrance Ba
- Yadda Jami’an Tsaro Suka Fara Gyara Wa ‘Yan Jari Bola Zama A Abuja…
Hukumar ta jaddda cewa, sauyawa zuwa yin amfani da tsarin tantance manyan motocin da ke shiga cikin Tashar, shi ne, kawai za a rinka yin amfani da shi, wajen barin manyan motocin shiga cikin Tashar.
Sanarawr ta kuma kara da cewa, daukacin manyan motocin da za su shiga cikin Tashar, dole su kasance suna dauke da shedar lambar motocin su a jikinsu, domin bin bukatar ka’idar da Hukumar ta gindaya.
“Duba da sabunta bin ka’idar shigar manyan motocin cikin Tashar, Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta amince da wasu sauye-sauye, domin a ciki gibin da ake dashi na ka’idojin Hukumar da take da sun a shiga cikin Tashar.” Inji Sanarwar.
“Wannan sauye-sauyen an yi su ne, bisa manufar bin ka’idar shigar cikin Tashar, musamman domin a dakile satar hanyar shiga cikin Tashar ga manyan motocin da ba su gabatar da takardun shedar ka’idar shiga cikin Tashar ba.” Acewar Sanarwar.
Kazalika, Hukumar ta NPA, ta bayar da umranin da a gaggauta wanzr da sauyin, biyo bayan sauya wadannan sabbin matakan da Hukumar ta yi, wanda za su fara aiki a cikin watan Fabirairun 2025.
“Bisa wannan sauyin, daga yanzu daukacin manyan motocin da suka tunkaro domin shiga cikin Tashar, dole su kasance suna sanye da lambar manyan motocin, domin bin ka’idojin da Hukumar ta gindaya.” Inji Sanawar.
“Dole ne manyan motocin su manna kwafin takardun shedar bayar bayar da kariya wato MSS, a jikin Gilsan manyan motocin su da ke nuna alamar cewa, an yarje masu shiga cikin Tashar.” A cewar Sanarwar.
“Daga yanzu gabatar zallar shedar lambar motocin a kofar shiga Tashar, Hukumar ba za ta sake lamuntar hakan ba.” Inji Sanawar.
“Sauyin bin ka’idar za ta fara aiki ne, daga ranar 3 ga watan Fabirairun 2025, kuma Hukumar ta umarci masu hada-hadar zirga-zirgar manyan motoci a Tashar da sauran masu ruwa da tsaki, da su tabbatar da sun kiyaye wannan ka’idojin, ko kuma Hukumar, ta kakaba masu takunkumi.” Inji Sanawar.