Shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya NPA Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana cewa, Hukumar na kan aiki da Hukumar Kwastam ta Kasa NCS domin sauyawa injin tantance Jiragen Ruwa da ke Apapa zuwa domin a a samu saukin sauke kayan da Jiragen suka yi jigilar kaya.
Dantsoho ya sanar da cewa, aikin bayan neman sahalewar da Ministan Bunksa Tattalin Arziki na Teku Adegboyega Oyetola ya samo ne daga Majalisar Zarwara ta Kasa domin sake aikin gina TinCan Island da sake yiwa Tashar ta Apapa garanbawul.
- Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
- Yadda Ake Ayyukan Gina Ababen More Rayuwa A Jihar Zamfara
Ya bayyana hakan ne, a ranar Talata a yayin da ya kai ziyarar aiki ta bazata domin duba aikin hanyar Tashar da ke a jihar Legas.
Ya ce, zai ci gaba da kai irin wannan ziyarar aikin ta bazata domin a tabbatar da cewa, ana bin ka’idar aikin domin samu sakamako mai kyau.
“Aikin na titin ya kasance, tamkar irin na sauran kasashen duniya kuma manufarsa shi ne, domin a rage cunkuso da ke faruwa Tashar.”
Shugaban Rukunonin Kamfanin Flour Mills Mista John Coumantaros ne, ya tarbi Dantsoho, a lokacin ziyarar aikin, inda suka tattauna kan ci gaban da ake ci gaba da samu da kuma yadda za a mayar da hankali, wajen zuba hannun jari kan aiki, musamman domin Tashoshin Jiragen Ruwan, su raba.
A na sa martanin Dantsoho, ya bayyana cewa, wannan ci gaban mai alfanu, ya yi daidai da sahalewar Gwamnatin Tarayya na aikin bunkasa kasuwanci wato NSW.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp