A ranar Asabar ne kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta doke Katsina United a gidanta da ci 1- 0 a wasan mako na biyu na gasar Firimiyar Najeriya (NPL).
Dan wasan Pillars Mustapha ne ya jefa kwallo a minti na 27 da fara wasan.
- An Rufe Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Asiya Karo Na 19 A Hangzhou
- 2034: Nijeriya Na Goyon Bayan Saudiyya Ta Dauki Nauyin Kofin Duniya
Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi bayan tashi wasan, kocin Pillars, Maikaba, ya yaba wa ‘yan wasansa wadanda ya ce, sun taka rawar gani.
Maikaba ya bayyana sakamakon wasan a matsayin mai albarka bayan da suka yi nasara da ci 1-0.
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Katsina United, Tope Bulus, ya ce kungiyarsa za ta dawo da karfinta domin lashe sauran wasannin da ke gabanta.
Ya kuma yabawa tawagarsa bisa jajircewarsu duk da cewar sunyi rashin nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp