Hukumar Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta dakatar da zirga-zirgar jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan wani jirgi ya yi hatsari a ranar Talata.
Shugaban NRC, Kayode Opeifa, ya shaida wa ’yan jarida a Abuja cewa babu jirgin da zai sake tashi har sai an kammala bincike kuma an tabbatar da tsaro.
- PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro
- Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?
Ya ƙara da cewa an riga an mayar wa fasinjojin da abin ya shafa kuɗin tikitinsu.
Opeifa ya bayyana cewa injiniyoyin NRC, jami’an hukumar binciken tsaro ta NSIB, da sauran hukumomi suna wajen da hatsarin ya faru domin gano musabbabin lamarin da kuma ɗaukar matakan kariya a nan gaba.
Ya kuma ƙaryata raɗe-raɗin cewa ana sakaci wajen kula da jiragen ƙasa, yana mai cewa hukumar koyaushe tana bin ƙa’idojin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp