• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NSA Ta Yiwa Jami’ar NPU Kutse Ta Yanar Gizo

by CMG Hausa
2 years ago
NSA

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

Kwanan baya, an samu babban ci gaba wajen bin bahasin batun kutsen da aka yiwa jami’ar masana’antu ta Arewa maso yammacin kasar Sin wato Northwestern Polytechnical University NPU a Turance ta yanar gizo, inda kasar Sin ta yi nazari kan wata manhaja, tare da tabbatar da yadda ma’aikatan hukumar kula da tsaron kasar Amurka wato NSA ke da hannu cikin batun. Lamarin ya kasance a matsayin wata shaida da ke nuna cewa, gwamnatin Amurka ta yiwa wasu kasashe kutse ta yanar gizo.

A daidai wannan lokaci, ma’aikatar tsaron Amurka ta kaddamar da takaitaccen bayani kan manyan tsare-tsaren yanar gizo na shekarar 2023, inda ta sake baza kalaman “kasar Sin na haifar da barazana”. Yayin da Amurka take satar bayanan sirrin kasar Sin ta hanyar manhajar musamman, ta kuma dora wa kasar Sin laifin, abin da take yi ya nuna cewa, tana mayar da kasar Sin a matsayin babbar abokiyar takararta. Bugu da kari, yayin da karfin shugabancin ‘yan siyasar Amurka ya ragu, suna kokarin baza kalaman “wasu na haifar da barazana” don karkatar da hankulan mutane. A sa’i daya kuma, hakan ya baiwa Amurka wani uzuri na cin zarafin kasar Sin ta fuskar yanar gizo da masana’antun sadarwa, wanda hakan ya share mata hanya ta kara yin kutsen yanar gizo a kasashen waje.

Yadda aka samu babban ci gaba wajen bin bahasin batun yi wa jami’ar NPU kutsen ta yanar gizo, ya nuna cewa, kasar Sin na da karfin kare kanta daga kutsen yanar gizo daga ketare, tana kuma da aniyar kiyaye tsaron yanar gizo a duniya. An yi imanin cewa, sakamakon kyautatuwar kwarewar kasashen duniya ta fuskar tsaron kansu a yanar gizo, ya sa za a sa aya kan yadda Amurka take yin danniya a yanar gizo. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin
Daga Birnin Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a
Daga Birnin Sin

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
Next Post
Japan

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Hukumar Kula Da Hakkin Bil Adam Ta MDD Kan Batun Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Ta Japan

LABARAI MASU NASABA

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025
Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

October 29, 2025
Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.