Hukumar tsaro ta NSCDC, a babban birnin tarayya, Abuja, za ta gurfanar da wasu mutane bakwai da ake zargi da lalata muhimman ababen more rayuwa a birnin.
Kwamandan rundunar na Abuja, Olusola Odumosu, ya bayyana haka a lokacin da yake baje kolin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Abuja.
- Adadin Kudin Ajiyar Sin Na Ketare Ya Ragu Zuwa Dala Tiriliyan 3.2024
- Masu Hidima Ga Kasa Kusha Kuriminku, An Kusa Fara Biyan N77,000 Duk Wata – Shugaban NYSC
Odumosu ya ce an kama biyar daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin ne yayin da suke cire murafan kwalbatin magudanar ruwa da igiyoyin wutar lantarki a birnin.
Ya ce, an kama mutanen biyar ne da tsakar dare, wadanda shekarunsu ke tsakanin shekaru 19 zuwa 24.