Ƙungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa naɗin da aka yi masa na mataimaki na musanman a ɓangaren yaɗa labarai ga shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON), Abdullahi Usman Saleh.
A matsayinsa na ɗan asalin jihar Kano, ɗaukaka darajar Malam Ahmad Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari ne ga masu aikin jarida a jihar.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe
- Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe
Naɗin nasa ya nuna irin ƙwarewarsa da sadaukarwarsa a ɓangaren yaɗa labarai da yake da shi.
Mu’azu kafin wannan muƙamin ya yi aiki a Sashen Hulda da Jama’a na Sashen Yaɗa Labarai na NAHCON, inda ya nuna ƙwarewa ta musamman da kuma sadaukar da kai a aikinsa na hulda da jama’a. Muna da yaƙinin cewa, ƙwarewarsa za ta kara inganta harkar yaɗa labarai a NAHCON, tare bunƙasa harkokin yaɗa labarai a hukumar.
Ƙungiyar NUJ reshen jihar Kano, ta yi murnar wannan muƙami tare da kwaɗaitar da Malam Mu’azu da ya ci gaba da kare martabar aiki tare da nuna ƙwazo da himma a sabon aikin nasa.