Kungiyar ‘yan jarida ta Kasa ta bayyana kisan gillar da aka yi wa wakilin gidan rediyon Muryar Nijeriya, Hamisu Danjibga a gidansa da ke Gusau abun takaici ne, kuma tayi kira ga Jami’an tsaro da su gaggauta zakulo wadanda suka yi kisan domin a hukunta su.
Kungiyar ta yi kira ga hukumomin tsaro a jihar da su binciki lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ta fito daga sakataren kungiyar na jihar, Ibrahim Ahmad Gada da yammacin Laraba a Gusau.
“Marigayi Hamisu Danjibga dan jarida ne, wakilin Muryar Nijeriya (VON) wanda aka tsinci gawarsa a cikin masai a bayan gidansa bayan kwana uku da batar shi”.
Kungiyar na mika ta’aziyya ga iyalai, da Muryar Nijeriya da daukacin al’ummar jihar Zamfara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp