Kungiyar malamai ta Nijeriya NUT reshen jihar Kaduna, ta yabawa gwamnatin gwamna Nasir El-Rufai bisa mayar da malaman makarantun gwamnati 1,288 da aka kora a baya bayan kammala jarabawar tantancewa.
Cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Afrilu 5, 2023 mai lamba NUT/GO/G7/Vol 4/732 mai dauke da sa hannun sakataren jihar, Adamu Ayuba Kaltungo, kungiyar ta yaba da irin wannan karamci da aka yi wa ’yan uwa masu girma da wannan lamarin ya shafa.
- Gwamnatin Kaduna Ta Sake Sallamar Malaman Makaranta 2,357 Daga Aiki
- El-rufa’i Zai Dauki Malamai 10,000 Bayan Sallamar 2,000 Daga Aiki
NUT ta ce mayar da su bakin aikin zai taimaka matuka gaya wajen cike gibin da ake samu tsakanin malamai da dalibai a bangaren makarantun firamare na gwamnati.
Idan dai ba a manta ba hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna (KADSUBEB) ta kori malaman firamare 2,357 sakamakon jarrabawar da suka yi a watan Yunin 2022, inda ta bayyana cewa an kori malamai 2,192 saboda rashin cin jarabawar.
A watan Afrilun da ya gabata, KADSUBEB ta dawo da korarrun malamai 1,288, bisa hujjar cewa ‘’ bayan tantancewa tare da tabbatar da kokensu, gwamnatin jihar ta amince da mayar da malamai 392, wadanda suka rubuta kuma suka ci jarabawar.