• English
  • Business News
Tuesday, July 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwagwarmayar Kwato Wa Ma’aikata Hakkinsu A Nijeriya

by Leadership Hausa
2 years ago
in Manyan Labarai
0
Gwagwarmayar Kwato Wa Ma’aikata Hakkinsu A Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A daidai lokacin da Nijeriya ta shiga sahun sauran kasashen duniya wajen bikin ranar ma’aikata ta duniya, yana da matukar muhimmanci mu yi nazari a kan hakki da gwagwamaryar ma’aikata a Nijeriya zuwa yanzu. Ranar ba wai ana nufin kawai a bayar da hutu ba ce a kuma yi fareti da bukukuwa kawai ba ne, ranar ce ta duba gudummawar ma’aikata da sadaukarwar da suka yi wajen gina kasa kuma gashi suna ci gaba da bayar da gudummawar ganin kasa ta samu ci gaban  da ake bukata.

Ya kamata al’umma su fahimmaci cewa, ranar ma’aikata ko kuma kamar yadda wasu ke kiranta da suna ‘May Day’ ya samo asali ne daga kungiyoyin gwagwarmayar nema wa ma’aikata hakkokinsu. Ranar ta samo asali ne daga kasar Amurka a karni na 19 tun daga wancan  lokaci kuma ake bukukuwan ranar a fadin duniya gaba daya.

  • Sin: Kasashen G7 Suna Wakiltar Sabawa Ka’idojin Kasa Da Kasa
  • Wasu Ke Neman Bata Mana Suna Kan Rikicin Shugabancin APGA – INEC

A Nijeriya an fara bikin ranar ne a shekarar 1980, bayan da gwamnatin soja ta Janar Olusegun Obasanjo ta ayyana ranar a matsayin ranar hutu.

A tsawon shekaru, ma’aikatan Nijeriya sun yi gwagwamarya daban-daban ta neman hakkokinsu wadanda suka hada da hakkin kafa kungiya da hakkin nemawa kansu hakkokinsu a kungiyance, da hakkin kariya daga cuttutuka a wajen aiki da bukatar a samar masu da mafi karancin albashi don su samu gudanar da aiki a cikin kwanciyar hankali.

Amma kuma a ra’ayin wannan jaridar har zuwa yanzu ba dukkan ma’aikatan Nijeriya ke amfana da wadannan hakkokin ba, da yawa daga cikin ma’aikatan Nieriya na ci gaba ne da fuskantar matsaloli da suka hada da rashin albashi mai inganci da kuna yadda ake nuna masu bambanci da kuma yadda suke aiki a cikin yanayi mai cutar da rayuwarsu.

Labarai Masu Nasaba

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

Tabbas batun mafi karancin albashi shi ne lamari mafi girma a cikin matsalolin da ma’aikata suke fuskanta a Nijeriya. Jihoji da dama sun kasa biyan albashin ma’aikata. Wani rahoto na wata kungiya mai zaman kanta mai suna BudgIT, ta bayyana cewa a shekarar da ta wuce akawai jihohi 12 daga cikn jihohi 36 da muke da su na kasa akalla sun kasa biyan ma’aikata albashin daya ko biyu, wasu jihohin ma bashin da ma’aikata ke bin su na albashi da ya wuce na wata 6 wasu na bin bashin albashin fiye da shekara 3.

Wannan kuma yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu gwamnanoni ke kaddamar da wasu manyan ayyukan da babu yadda za a iya yinsu suna kuma zartar da kasafin manyan kudaden da za a rinka biyansu bayan in sun yi ritaya, ba za mu amince da wannan lamarin ba.

Gwamnatin tarayya na shirin cire tallafin man fetur wanda hakan kuma zai kara tsawalla tsadar kayan masarufi da harkokin rayuwar yau da kullun ta al’umma, a kan haka ne ya dace, gwamnati mai jiran kama madafun iko ta Bola Hamed Tinubu ta kara wa ma’aikata albashi tare da sauran abubuwan da za su rage radadin da za a shiga sakamakon cire tallafin man.

Wannan jaridar ta nuna kyamarta a kan yadda kungiyoyin ma’aikata ke shiga yajin aiki daga an samu wata takaddama, muna kuma godiya ga gwmanatin tarayya a kan yadda ta fara cika wa ma’aikatan alkawurransu, a ra’ayinmu, rajin aiki ya zama wani tsohon yayi, ya kuma kamata gwamnatin tarayya ta tabbatar da tana cikia dukkan alkawarin da ta dauka a tsakaninta da kungiyoyin kwadago a kowane lokaci.

Babu tantamamr cewa, babbar matsalar da ma’aikatan Nijeriya ke fuskanta a wannann lokacin ita ce ta rashin tabbas a wurin ayyukansu. Ma’aikata da dama a bangaren kamfanoni masu zaman kansu ana daukar su ne ba a tsarin dindindin ba, basu da wani tsari na taimaka wa rauyuwar su bayan sun ajiye aiki, kamar tsarin fansho da inshorar lafiya, wanda hakan yana cutar da rayuwarsu bayan sun tsufa sun ajiye aiki.

Wata matsalar da ma’aikata  Nijeriye ke fuskanta ya hada da yadda ake nuna masu bambanci, musamman bambancin da ake nuna wa mata. Mata na cikin kaso mafi yawa na ma’aikatan Nijeriya amma suna fuskantar barazana da tsagwama a wuraren aikinsu.

Duk da wadannan  kalubalen, ma’aikata a Nijeriya na ci gaba da fafutuka neman hakokkinsu ta hanyoyoin kungiyoyin NLC da TUC, sun ci gaba da gwagwarmayar nema wa ma’aikata hakkokinsu da suka hada da albashi mai tsoka da yanayin aiki mai kyau ba tare da takura ba, sun kuma taka rawar gani a kokarin yaki da nuna bambaci a tsakanin mata, ta yadda kowa za iya aiki a cikin walwala ba tare da fargaba ko wata takura ba.

Ya zama dole mu ci gaba da mutumtawa tare da tuna gudummawar da ma’aikata suka bayar a wajen tabbatar da mutuncin ma’aikata a fadin duniya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Kwato 'YanciMa'aikata
ShareTweetSendShare
Previous Post

NUT Ta Yabawa El-Rufai Kan Dawo Da Korarrun Malaman Makaranta 1,288 Bakin Aiki

Next Post

ISWAP Sun Kashe ‘Yan Gudun Hijira 3 Da Raunata Sojoji 8 Da Wasu 5 A Borno

Related

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
Manyan Labarai

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

6 hours ago
Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara
Manyan Labarai

Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

8 hours ago
Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina
Manyan Labarai

Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina

19 hours ago
Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Ta’adda Mai Dada
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Ta’adda Mai Dada

1 day ago
Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki
Manyan Labarai

Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki

2 days ago
Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa
Manyan Labarai

Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

2 days ago
Next Post
Kwamandojin ‘Yan Ta’adda, Ba’a Usman, Alhaji Ari, Da Wasu Da Dama Sun Mika Wuya Ga Sojoji

ISWAP Sun Kashe ‘Yan Gudun Hijira 3 Da Raunata Sojoji 8 Da Wasu 5 A Borno

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

June 30, 2025
Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

June 30, 2025
Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

June 30, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

June 30, 2025
Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

June 30, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

June 30, 2025
Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

June 30, 2025
CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

June 30, 2025
Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku

Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku

June 30, 2025
Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

June 30, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.