Hukumar Ci gaban Arewa maso Yamma (NWDC) ta bayyana cewa tana shirin sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanonin Shanghai Integrated Infrastructure Development Limited da Pearless Advisory Limited domin saka hannun jari na kusan dala miliyan 200 a fannin noma.
Wannan shirin zai mayar da hankali kan bunƙasa noma na zamani, da kiwo, da kuma tabbatar da Nijeriya ta zama jagora a harkar kiwon dabbobi a duniya.
- Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwaÂ
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Bayar Da Kiwon Lafiya Kyauta Ga ‘Yan Fansho Masu Karamin KarfiÂ
Shugaban hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ya ce wannan shiri ya yi daidai da umarnin Shugaba Bola Tinubu na buɗe damar noma a yankin Arewa maso Yamma. Ya bayyana cewa hukumar za ta yi amfani da wannan jarin wajen horar da matasa sama da miliyan bakwai a fannin aikin gona, tare da mayar da su masu samar da dogaro da kai ta hanyar noma da kiwo.
Farfesa Ma’aji ya jaddada cewa an kafa tsarin gaskiya da riƙon amana domin amfani da jarin yadda ya dace. Ya ƙara da cewa gwamnati za ta samar da yanayin da ya dace domin jawo hankalin masu saka hannun jari, tare da sauƙaƙe musu domin ci gaban harkokin kasuwanci.
A nasa jawabin, mai gudanar da harkokin Pearless Advisory Limited, Kunle Dawodu, ya yaba da damar haɗin gwuiwar tare da hukumar, inda ya ce shirin zai fi karkata ga noma na zamani da fasahar kere-kere daga ƙasar Sin. Ya bayyana cewa wannan zuba jari ba zai amfanar da hukumar da kamfanoni kaɗai ba, har ma zai ƙara wa Nijeriya damar tabbatar da tsaron abinci da kuma bunƙasa fitar da kayayyaki ba man fetur ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp