Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) reshen Bauchi, ta bayyana sauya wurin da za a fara gudanar da kwas din rukunin ‘B’ sahu na II, na ‘yan bautar ƙasa wanda za a soma daga Laraba 28 ga watan Agusta zuwa Talata 17 ga Satumba, 2024 ga waɗanda aka tura zuwa 2024 jihar.
Za a karbi bakuncin ‘yan bautar ƙasar ne a Kwalejin ilimi na Adamu Tafawa Balewa da ke Kangere, a wajen babban birnin jihar, sakamakon aikin gyare-gyaren da ake yi a sansanin dindindin na Wailo NYSC da ke kan hanyar Bauchi zuwa Maiduguri.
- NYSC Ta Kori Ƴan Bautar Ƙasa 54 Masu Takardun Bogi
- Ana Fargaba An Sha Kwana Da Shinkafar Gwamnatin Tarayya A Bauchi, Gombe, Da Dutse
Ko’odinetan NYSC na jihar Bauchi, Rifkatu Daniel Yakubu, ce bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Bauchi yau Litinin.
Ta yi bayanin cewa sauyin wurin ya zama dole don sauƙaƙe aikin gyaran sansanin na dindindin inda ta ƙara da cewa kimanin wanda za su yi bautar ƙasa 1,900 aka tura jihar don gudanar da atisayen rukunin ‘B’ sahu II na shekarar 2024 jihar ta Bauchi.