Ofishin da ke kula da ‘yan fasho na jihar Kaduna karkashin jagorancin Farfesa Salamatu Idris Isah, ya bayyana cewa, Ofishin ya fitar da sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin, inda za a fara tantance su a shiyyoyi Uku da ke fadin jihar.
Farfesa ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis a ofishinta yayin da ta ke zantawa da manema labarai kan shirin fara tantance ma’aikatan da za su ci gajiyar shirin.
- Mutane 195 Isra’ila Ta Kashe A Harin Sansanin Jabalia Da Ke Gaza
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Cikakken ‘Yancin Kan Kasar Sudan
Don haka, wadanda ke cikin shiyya ta biyu (kwaryar jihar Kaduna) za a tantance su a ofishin kula da ‘yan fashon da ke Katuru Road, Badarawa GRA, inda za a fara aikin tantancewar a fadin jihar baki daya a ranar 8 zuwa 15 ga watan Nuwamba, 2023.
Wadanda aka tantancen za su fara jin makudan kudadensu a asusun ajiyarsu na banki daga ranar 18 ga watan Nuwamban.
Tsarin biyan, an kasa shi ne zuwa tsoho da sabon tsari: a karkashin tsohon tsari a bangaren ma’aikatan jiha, wannan shi ne rukuni na 22 yayin da a bangaren ma’aikatan kananan hukumomi ya kasance rukuni na 20. A bangaren sabon tsari, wannan shi ne rukuni na 51.
Farfesa ta kara da cewa, ofishin ya shirya biyan tsoffin ma’aikatan 1,051 inda aka ware tsoffin ma’aikata a tsohon tsari na jiha 331, sannan na kananan hukumomi su 542. A sabon tsari, an ware tsoffin ma’aikatan su 178.
Bugu da kari, hukumar ta kasafta kudin da gwamnan ya fitar zuwa gida biyu, inda aka ware Naira Biliyan N2,600,000 don biyan tsoffin ma’aikatan da ke kan tsohon tsarin, ragowar Naira Miliyan N500,000 aka sanya shi don biyan tsoffin ma’aikatan da ke kan sabon tsari.
Farfesa, da take amsa tambaya kan masu korafin cewa, ba su ga sunansu ba, ta ce, “su yi hakuri ba a zo kansu ba ne, sunayen a tsare suke, ba a tsallake, don haka, ba za a tsallake kowa ba.”
A karshe ta yi gargadi ga masu cin gajiyar shirin kan cewa, Hukumar bata nada kowa ba kan ya amsa sisi ko kobo da nufin shiga tsarin amsar kudin fansho da garatuti, “hakkinku ne kuma dole a baku.”