Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Abuja ya yi karin haske game da rahotannin da kafafen yada labarai suka fitar kan soke bizar ‘yan Nijeriya 264.
Ofishin Jakadancin ya tabbatar da cewa, Fasinjojin ba su cika sharudda daidai da bukatun ka’idodin Masarautar ba ne.
- Yanzu-yanzu: Saudiyya Ta Soke Bizar ‘Yan Nijeriya 264 Bayan Sun Isa Jeddah
- Ranar ‘Yancin Kai: Tinubu Ya Bar Saudiyya Zuwa Guinea Bissau
“Fasinjojin sun gabatar da bayanan da ba daidai ba don samun wata nau’in biza wacce ba ta halatta a garesu ba, wanda aka gano a lokacin da suka isa kasar Saudiyya.
“Ofishin Jakadancin Masarautar Saudiyya na son jaddada muhimmancin bin ka’idoji da dokokin da masarautar Saudiyya ta kafa ga duk masu ziyara. Don haka, duk fasinjoji ya kamata su sake duba duk takaddun tsarin masarautar don sanin daidaitattun sharuddan Masarautar kafin su tashi daga ƙasashensu zuwa Masarautar. Wannan tsari bai takaita ga ‘yan Nijeriya kadai ba, har da sauran ‘yan kasashe daban”.
In ba a manta ba, a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba, mun rahoto muku yadda masarautar Saudiyya ta soke bizar ‘yan Nijeriya 264 jim kadan bayan isarsu kasar Saudiyya domin ziyara a jirgin Air Peace wanda ya tashi daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano bayan ya taso daga Lega a daren Lahadi.