Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Abuja ya gudanar da bikin tunawa da ranar kafa kasar ta Saudiyya karo na 94 a gidan jakadan kasar, Faisal bin Ebraheem Alghamdi.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin ofisoshin diflomasiyya, wakilan kungiyoyin duniya da sauran manyan ‘yan kasuwa.
- Tarihin Ci Gaban Sin: Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa
- Ƴan Ta’adda Sun Lalata Wutar Lantarkin Maiduguri Zuwa Damaturu
Da yake jawabi, Ambasada Alghamdi ya bayyana muhimmancin bikin, wanda ke nuna cika shekaru 94 da kafa Daular kasar ta Sarki Abdulaziz bin Abdulrahman Al Saud, wacce ta yi tsayin daka bisa tsarin akidar Musulunci da kiyaye dabi’u na daidaito, adalci, da amana.
Ya jaddada cewa, Masarautar Saudiyya ita ce ta farko a cikin daulolin da aka kafa a yankin Gabas ta Tsakiya wacce ta zamo abin koyi, inda hakan ke nuni da irin ci gaban da ta samu.
Ambasada Alghamdi ya kuma yi amfani da damar wajen nuna farin ciki da dadaddiyar alakar da ke tsakanin Saudiyya da Nijeriya, wadda take samun ci gaba tun bayan kafuwarta sama da shekaru 63.
Bugu da kari, Ambasada Alghamdi ya bayyana jajircewar Saudiyya wajen tabbatar da annashuwa da kwanciyar hankalin mahajjata da masu Umurah, inda a shekarar 2023, Masarautar ta bai wa ‘Yan Nijeriya 120,000 damar zuwa aikin Umrah da kuma masu zuwa aikin Hajji su 65,000.
Bugu da kari, Jakadan ya bayyana cewa, Masarautar Saudiyya ta bayar da tallafin karatu ga daliban Nijeriya maza da mata 260, wanda hakan ya kara habaka musayar ilimi a tsakanin kasashen biyu. Ya kuma bayyana cewa, yawan cinikin da ke tsakanin Saudiyya da Nijeriya ya habaka zuwa dala miliyan 600.
Ambasada Alghamdi ya kuma tabo zancen ayyukan jin kai da Masarautar take yi a Nijeriya, ciki har da aikin sa kai na Nur-Saudi wanda kashi na farko ya mayar da hankali a kan magance cutar makanta da yoyon fitsari da kuma ciwon zuciya.
“Daya daga cikin muhimman abubuwan da Masarautar ta samu a fannin jinya a Nijeriya shi ne nasarar raba wasu tagwayen Nijeriya da aka yi a watan Mayu, wanda hakan wani muhimmin ci gaba ne a bangaren likitocin Saudiyya.
“Wannan tiyatar ita ce tiyatar raba mutane ta 56 wadda likitocin Saudiyya suka yi, kuma har yanzu kasar Saudiyya na daya daga cikin manyan kasashen duniya wajen gudanar da irin wadannan ayyuka masu sarkakiya.” In ji shi.
Jakadan ya kuma yi karin haske kan burin Saudiyya na 2030, da shirin kawo sauyi na duniya da ke neman samar da al’umma mai alfanu, da gina tattalin arziki da kuma qasa mai kishi.
Ambasada Alghamdi ya tabbatar da cewa Masarautar kasarsu ta himmatu wajen samar da damammaki ga ‘yan kasarta da abokan huldarta na duniya ciki har da Nijeriya, ta wannan hanya ta hangen nesa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp