• English
  • Business News
Saturday, July 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ofishin Jakadancin Saudiyya Ya Yi Bikin Cikar Daularsu Shekaru 94 Tare Da Karfafa Alaka Da Nijeriya

by Abdulrazaq Yahuza and Sulaiman
10 months ago
in Labarai
0
Ofishin Jakadancin Saudiyya Ya Yi Bikin Cikar Daularsu Shekaru 94 Tare Da Karfafa Alaka Da Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Abuja ya gudanar da bikin tunawa da ranar kafa kasar ta Saudiyya karo na 94 a gidan jakadan kasar, Faisal bin Ebraheem Alghamdi.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin ofisoshin diflomasiyya, wakilan kungiyoyin duniya da sauran manyan ‘yan kasuwa.

  • Tarihin Ci Gaban Sin: Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Ƴan Ta’adda Sun Lalata Wutar Lantarkin Maiduguri Zuwa Damaturu

Da yake jawabi, Ambasada Alghamdi ya bayyana muhimmancin bikin, wanda ke nuna cika shekaru 94 da kafa Daular kasar ta Sarki Abdulaziz bin Abdulrahman Al Saud, wacce ta yi tsayin daka bisa tsarin akidar Musulunci da kiyaye dabi’u na daidaito, adalci, da amana.

Labarai Masu Nasaba

A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba

Ya jaddada cewa, Masarautar Saudiyya ita ce ta farko a cikin daulolin da aka kafa a yankin Gabas ta Tsakiya wacce ta zamo abin koyi, inda hakan ke nuni da irin ci gaban da ta samu.

Ambasada Alghamdi ya kuma yi amfani da damar wajen nuna farin ciki da dadaddiyar alakar da ke tsakanin Saudiyya da Nijeriya, wadda take samun ci gaba tun bayan kafuwarta sama da shekaru 63.

Saudiyya

Bugu da kari, Ambasada Alghamdi ya bayyana jajircewar Saudiyya wajen tabbatar da annashuwa da kwanciyar hankalin mahajjata da masu Umurah, inda a shekarar 2023, Masarautar ta bai wa ‘Yan Nijeriya 120,000 damar zuwa aikin Umrah da kuma masu zuwa aikin Hajji su 65,000.

Bugu da kari, Jakadan ya bayyana cewa, Masarautar Saudiyya ta bayar da tallafin karatu ga daliban Nijeriya maza da mata 260, wanda hakan ya kara habaka musayar ilimi a tsakanin kasashen biyu. Ya kuma bayyana cewa, yawan cinikin da ke tsakanin Saudiyya da Nijeriya ya habaka zuwa dala miliyan 600.

Ambasada Alghamdi ya kuma tabo zancen ayyukan jin kai da Masarautar take yi a Nijeriya, ciki har da aikin sa kai na Nur-Saudi wanda kashi na farko ya mayar da hankali a kan magance cutar makanta da yoyon fitsari da kuma ciwon zuciya.

“Daya daga cikin muhimman abubuwan da Masarautar ta samu a fannin jinya a Nijeriya shi ne nasarar raba wasu tagwayen Nijeriya da aka yi a watan Mayu, wanda hakan wani muhimmin ci gaba ne a bangaren likitocin Saudiyya.

Saudiyya

“Wannan tiyatar ita ce tiyatar raba mutane ta 56 wadda likitocin Saudiyya suka yi, kuma har yanzu kasar Saudiyya na daya daga cikin manyan kasashen duniya wajen gudanar da irin wadannan ayyuka masu sarkakiya.” In ji shi.

Jakadan ya kuma yi karin haske kan burin Saudiyya na 2030, da shirin kawo sauyi na duniya da ke neman samar da al’umma mai alfanu, da gina tattalin arziki da kuma qasa mai kishi.

Ambasada Alghamdi ya tabbatar da cewa Masarautar kasarsu ta himmatu wajen samar da damammaki ga ‘yan kasarta da abokan huldarta na duniya ciki har da Nijeriya, ta wannan hanya ta hangen nesa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Tarihin Ci Gaban Sin: Abin Koyi Ga Kasashe Masu Tasowa

Next Post

Sin Ta Samu Karuwar Mazauna Birane Cikin Shekaru 75

Related

A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya
Labarai

A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

5 hours ago
Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano
Labarai

Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba

5 hours ago
Kasar Sin Ta Nuna Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Nijeriya Buhari
Labarai

Za A Dinga Tunawa Da Buhari A Matsayin Waliyyi A Siyasar Nijeriya —Dakta Zangina

6 hours ago
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Manyan Labarai

Tinubu Ya Nada Ɗan Babangida A Matsayin Shugaban Bankin Manoma

7 hours ago
‘Yan Kasuwa Na Shirin Yi Wa Dangote Zanga-zanga Kan Rage Farashin Gas
Labarai

‘Yan Kasuwa Na Shirin Yi Wa Dangote Zanga-zanga Kan Rage Farashin Gas

7 hours ago
Lai Ching-Te Bai Cancanci Zama Jagoran Yankin Taiwan Ba
Ra'ayi Riga

Lai Ching-Te Bai Cancanci Zama Jagoran Yankin Taiwan Ba

8 hours ago
Next Post
Sin Ta Samu Karuwar Mazauna Birane Cikin Shekaru 75

Sin Ta Samu Karuwar Mazauna Birane Cikin Shekaru 75

LABARAI MASU NASABA

Dangote

Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA

July 18, 2025
Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

July 18, 2025
2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

July 18, 2025
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

July 18, 2025
majalisar kasa

Kirkirar Sabbin Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Dabaibaye Sauraron Jin Ra’ayoyin Gyaran Tsarin Mulki

July 18, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

July 18, 2025
Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

July 18, 2025
A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

July 18, 2025
Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano

Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba

July 18, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ta Kai Syria

July 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.