Ofishin jakadancin Sin dake Najeriya ya gudanar da liyafar murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin, jakadan Sin dake kasar Yu Dunhai da shugaban majalisar wakilan Najeriya Abbas Tajudeen sun halarci bikin tare da gabatar da jawabai.
Jakada Yu ya waiwayi ci gaban da Sin ta samu a cikin wadannan shekaru 75 da suka gabata, kuma ya ce, wannan shi ne karo na da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya kai ziyarar aiki a kasar Sin bayan hawa karagar mulki, da ma halartar taron kolin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika, inda shugabanin kasashen biyu sun kai ga matsaya daya wajen daga huldar kasashen biyu zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, matakin da ya bude sabon babi na raya huldarsu. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa fiye da 10, don tabbatar da yin ingantaccen hadin gwiwa karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”.
- Sin Ta Kaddamar Da Gagarumin Bikin Ba Da Lambobin Yabo Na Kasar Sin
- Gwamnan Kano Ya Nada Hauwa Isah Ibrahim Manajan Daraktan ARTV
A nasa bangare, Tajudeen ya taya Yu murnar zama sabon jakadan Sin dake Najeriya, ya ce, sabuwar kasar Sin na samun bunkasuwa mai armashi a bangaren tattalin arziki da kimiya da fasaha da ma al’umma, tun kafuwarta a shekarar 1949, Sin kasa ce dake samun saurin bunkasuwa kuma jigon duniya wajen yin kwaskwarima, kuma karfinta na kara bayyanawa wajen dunkulewar duniya baki daya.
Tajudeen ya kara da cewa, Sin da Najeriya na zurfafa huldarsu bisa tushen mutunta juna. A gun taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudanar ba da dadewa ba, yarjejeniyoyin da shugabanin kasashen biyu suka kulla a gun taron, sun jaddada niyyar kasashen biyu na zurfafa huldarsu, wadanda suka samar da nagartacciyar hanya ga Najeriya wajen samun jari a wasu muhimman bangarori ciki har da samar da makamashi da kimiyya da sauransu. Majalisarsa za ta tsai da wasu dokoki don nuna goyon baya ga kokarin tabbatar da ci gaban da shugabanin suka samu a yayin taron. (Amina Xu)