• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ofishin Kula Da Harkokin Taiwan Na Majalisar Gudanarwa Da Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Sun Yi Tsokaci Kan Sakamakon Zabukan Taiwan

by CGTN Hausa
2 years ago
Taiwan

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

Mai magana da yawun ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Chen Binhua, ya yi bayani kan sakamakon zaben yankin Taiwan da yammacin jiya 13 ga wata, inda ya ce, sakamakon zabukan biyu a Taiwan ya shaida cewa, jam’iyyar Democratic Progressive Party wato DPP ba ta iya wakiltar muradun jama’ar yankin. Ya ce Taiwan, yanki ne da ba za’a iya ware shi daga kasar Sin ba, kuma zaben ba zai iya sauya babban tushe gami da alkiblar dangantakar Taiwan da babban yankin kasar Sin ba, kana ba zai iya sauya babban fatan al’ummomin bangarorin biyu na kara yin mu’amala da kusantar juna ba, kuma ba zai iya sauya makomarsu ba, wato tabbas za a samu dunkulewar kasar Sin baki daya.

A nasa bangare, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, harkokin Taiwan, harkokin siyasa ne na cikin gidan kasar Sin. Ya ce ba tare da la’akari da sauyawar halin da ake ciki a wurin ba, kasar Sin za ta kasance daya tak a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar, lamarin da ba za’a iya sauyawa ba. Ya ce gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasantuwar kasarta daya tak a duniya, da nuna adawa da masu yunkurin balle Taiwan daga babban yankin kasar, da nuna adawa da “kasancewar Sin guda biyu” da “Sin daban, Taiwan daban”, kuma ba za ta sauya wannan matsayi ba. Bugu da kari, kasa da kasa suna tsayawa kan ra’ayi daya na kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma hakan ba zai sauya ba.

An yi zabukan jagoran yankin Taiwan gami da wakilan jama’ar yankin na bana a jiya Asabar, inda sakamakon zabukan ya nuna cewa, ‘yan takarar dake karkashin tutar jam’iyyar DPP, Lai Ching-te da Hsiao Bi-khim sun zama jagora gami da mataimakiya. A cikin kujeru 113 na majalisar kafa dokokin yankin Taiwan kuma, jam’iyyar Chinese Kuomintang party ta samu guda 52, yayin da jam’iyyar DPP ta samu 51, kana jam’iyyar TPP ta samu guda 8, sai kuma ‘yan takara indipenda suka samu 2. (Murtala Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
Next Post
Kasar Sin Na Adawa Da Tsokacin Amurka Kan Zaben Yankin Taiwan

Kasar Sin Na Adawa Da Tsokacin Amurka Kan Zaben Yankin Taiwan

LABARAI MASU NASABA

Da Dumi-duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Ondo

Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5

November 10, 2025
Matatun mai

Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta 

November 10, 2025
Jibrin Kofa

Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC

November 10, 2025
Boko haram

Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno

November 10, 2025
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.