Fitaccen ɗan siyasa, Reno Omokri, da kuma wani shahararren mai amfani da kafar X, mai suna Sarki, sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, bai halarci jana’izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ba.
Omokri ya ce rashin zuwa wannan jana’iza zai iya zama matsala ga Obi idan yana fatan samun goyon bayan ’yan Arewa a zaɓen 2027.
- Kotu Ta Wanke Fayose Daga Zargin Zambar Naira Biliyan 3.3
- Yara 2 Sun Kuɓuta Bayan Shafe Shekaru 6 A Hannun Boko Haram A Borno
Ya bayyana hakan a matsayin rashin girmamawa ga mutanen Arewa da kuma shugabansu da ya rasu.
Sarki ma ya ce babu wani uzuri da zai hana Obi halartar jana’izar, musamman idan yana son a ɗauke shi a matsayin mutum mai neman haɗin kan Nijeriya.
Ya ce fitowar sauran shugabannin siyasa zuwa jana’izar ya nuna yadda suka daraja Arewa da iyalan Buhari.
Dukkanin su biyun sun bai wa Obi shawara da ya sake duba yadda yake tafiyar da siyasarsa, kuma ya ƙara ƙoƙari wajen kyautata alaƙa da mutanen Arewa, idan yana so ya yi nasara a babban zaɓe mai zuwa.
Sun ce irin wannan abu zai iya kawo cikas ga nasarar da yake fatan samu a siyasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp