Ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan mata ta Nijeriya, Asisat Oshoala, ta bayyana cewa gasar cin kofin Afrika ta mata da ake yi yanzu a Moroko, ita ce gasar ƙarshe da za ta buga wa ƙasar.
Asisat, mai shekaru 30, ta sanar da hakan ne a shafinta na Facebook, inda ta ce lokaci ya yi da za ta daina wakiltar Nijeriya domin ta bai wa sabbin matasa dama su ci gaba da haskakawa a duniyar ƙwallon ƙafa.
- Ban Tsani Buhari Ba, Ina Sukar Sa Ne Kawai Kan Matsalar Tsaro – Ortom
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Tsohuwar ‘yar wasan gaban ta Barcelona ta ce ta samu gagarumar nasara a rayuwarta ta ƙwallo, ciki har da lashe kyautar garzuwar ‘yar wasa a Afirka har sau shida (a shekarun 2014, 2016, 2017, 2019, 2022 da kuma 2023).
Ta ce: “Na gode da goyon bayan da kuka banni a tsawon waɗannan shekaru. Zan daina buga wa Nijeriya wasa, amma har abada ba zan manta da tutar ƙasar nan ba. Zan yi kewar lokutan da na shafe da tawagar Super Falcons.”
Asisat ta kasance gwarzuwar da ta ja hankalin duniya da ƙwarewarta, kuma abin koyi ce ga matasan ‘yan wasa mata a faɗin Afirka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp