Victor Osimhen, tauraro ɗan wasan gaba na Super Eagles da Napoli, na dab da komawa ƙungiyar Galatasaray ta ƙasar Turkiyya bayan wata kakar aro mai armashi da ya shafe a can. Rahotanni sun tabbatar da cewa Osimhen bai halarci atisayen farko na Napoli ba a ranar Litinin, yayin da ƙungiyar ke shirin fara sabuwar kakar wasa.
Osimhen ya bayyana takardar rashin lafiya domin uzurin rashin halarta, amma rahotanni daga ciki na nuna cewa yana ci gaba da tattaunawa da Galatasaray don komawa a matsayin cikakken ɗan wasa. A kakar bara, ya ci ƙwallaye 26 a wasanni 30, yana daga cikin manyan jiga-jigan da suka taimaka wa Galatasaray lashe gasar Super Lig karo na 25.
- Da Ɗumi-Ɗumi: Osimhen Ya Amince Da Komawa Galatasaray Na Dindindin
- De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City
Kocin Napoli, Antonio Conte, ya bayyana cewa ba ya da cikakken shiri da Osimhen a wannan sabon lokaci, yana mai cewa ƙungiyar ba za ta sayar da ɗan wasan ba sai an biya kuɗinsa mafi ƙaranci Yuro miliyan 75 (kimanin fam miliyan 64).
Duk da cigaban da aka samu a tattaunawar, har yanzu ana fuskantar ƙalubale wajen kammala cinikin. A gefe guda kuma, sabon ɗan wasan Napoli Kevin De Bruyne, wanda aka siya daga Manchester City, bai halarci atisayen ba duk da kasancewarsa cikin sabbin shirin ƙungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp